HomeSashen HausaZan Yi Aiki da Duk Wanda Zai Tsaftace Najeriya A Shekarar 2027...

Zan Yi Aiki da Duk Wanda Zai Tsaftace Najeriya A Shekarar 2027 – Inji Sule Lamido

-

Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma tsohon ministan harkokin wajen Najeriya, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana cewa, yana da buɗaɗɗen zuciya wajen mara wa kowace irin tsari baya a cikin jam’iyyar PDP ko wajen ta, muddin tsarin zai taimaka wajen tsare Najeriya da tabbatar da zaman lafiya a zaben 2027.

Nigerian Post ta samu cewa, Lamido ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Manema Labarai a birnin Kano a ranar Talata 22 ga watan Yuli 2025, inda ya ce, yana da cikakken imani da Najeriya. Don haka duk wani shiri, ko a cikin PDP ko a wajen ta, da zai taimaka wa tsaron Najeriya da ceto ƙasar na ganin ya bada goyan bayansa a shekarar 2027.

Sai dai ya musanta jita-jitar da ke yawo cewa yana shirin komawa jam’iyyar ADC, wanda ya jaddada cewa, har yanzu yana cikin jam’iyyar PDP, duk da cewa tana da matsaloli. Ya ce, ba zai iya gudu ya barta ya shigar wata ƙaramar jam’iyyar ADC ba.

Lamido ya tunatar da irin matsayin da PDP ta ba shi a baya, ciki har da na ministan harkokin waje da kuma gwamnan jihar Jigawa, yana mai cewa, ba zai iya watsi da jam’iyyar PDP ba wanda idan ya ce zai yi haka kamar ya ci amana ne.

Haka kuma, kan batun ƙirƙiro sababbin jihohi, Lamido ya bayyana cewa ko da yake wannan bukata na da halacci, hakan ba zai warware matsalolin Najeriya ba, wanda ya ce ƙirkiro sababbin jihohi ba zai magance rashin tsaro, yunwa, talauci ko rabuwar kai tsakanin Arewa da Kudu ba.

Dangane da ziyarar da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya kai wa Shugaba Bola Tinubu, Lamido ya ce Kwankwaso nada ‘yancin hakan, yana mai cewa babu laifi a irin wannan ziyara.

Lamido ya nuna cewa lokaci ya yi da ‘yan siyasa za su tsaya tsayin daka domin ceto Najeriya daga halin da ta shiga, tare da fifita maslahar kasa akan kowane irin bambancin siyasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Ɓarawo Ya Sace Motar Ayarin Mataimakin Gwamna A Gidan Gwamnatin Kano

Ɓarawo Ya Sace Motar Ayarin Mataimakin Gwamna A Gidan Gwamnatin Kano Wani barawon mota ya kutsa cikin Gidan Gwamnatin Kano da sanyin safiyar Litinin ya kuma...

‎Yansanda Sun Kama Masu Aikata Laifuka Daban-daban, Sun Ceto Mutane 47 da Aka Yi Garkuwa da Su a Jihar Katsina

Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Katsina ta bayyana cewa ta samu nasarori masu yawa a yakin da take yaki da laifuka, ciki har da kama mutanen...

Most Popular