HomeSashen HausaGwamnatin Tarayya Ta Ware Naira Biliyan 4.2 Don Bunkasa Bincike da Fasaha...

Gwamnatin Tarayya Ta Ware Naira Biliyan 4.2 Don Bunkasa Bincike da Fasaha a Makarantun Gaba da Sakandire.

-

Gwamnatin Tarayya ta amince da bayar da tallafin naira biliyan 4.2 ga ayyukan bincike 158 da ke karkashin Asusun Tallafawa Bincike na TETFund (NRF) na shekarar 2024. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na TETFund, Abdulmumin Oniyangi, ya fitar a Abuja. Ya ce tantancewar da kwamitin nazari da sa ido na TETFund (NRFS&MC) ya gudanar ya biyo bayan karɓar bayanan ra’ayi (concept notes) 6,944 daga masana daban-daban a fadin ƙasar.

A cikin adadin, bangaren Kimiyya, Fasaha da Kirkire-Kirkire (SETI) ya samu mafi yawan kudi da ya kai naira biliyan 2.34, yayin da bangaren Harsuna da Kimiyyar Zamani (HSS) ya samu naira biliyan 1.02, sai kuma ayyukan da suka hada fannoni da dama (Cross-Cutting) da aka ware musu naira miliyan 870.7. Manyan jami’o’in da suka fi cin gajiyar tallafin sun hada da Jami’ar Fasaha ta Minna da ke da ayyuka 15 da kudinsu ya kai naira miliyan 400.03, Ahmadu Bello University dake Zariya, da ayyuka 13 da kudin su ya kai naira miliyan 359.80, da Jami’ar Fasaha ta Akure da ke da ayyuka 12 da kudin su ya kai naira miliyan 341.60.

Wasu daga cikin muhimman ayyukan binciken sun hada da kirkirar takin zamani da ke dauke da sinadarai masu amfani daga tsirrai, da kuma samar da jirgi mai sarrafa kansa don magance ciyawa da cututtuka a gonakin masara da wake. Haka zalika, akwai kirkirar na’urar duba lafiya ya zamani don dakarun da ke filin daga.

A wani bangare na kokarin habaka kirkire-kirkire, gwamnati ta kuma amince da kafa cibiyoyin kirkire-kirkire da kasuwanci (Innovation and Entrepreneurship Hubs) guda 18 a makarantun da ke cin gajiyar TETFund a sassa shida na kasar nan. Wadannan cibiyoyi za su hada da dakunan gwaji irin su na lantarki, kirkirar kayayyaki, da na’urar robot da kuma fasahar Artificial Intelligence. Haka kuma, gwamnati ta ware kudade a cikin kasafin 2025 ga cibiyoyi 15 da suka hada da Jami’ar Dutse, Jami’ar Uyo, Jami’ar Ibadan da sauransu, inda kowane daga cikin su zai samu tsakanin naira miliyan 750 zuwa biliyan daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Bello Turji Ya Saki Mutane 32, Ya Amince Da Dakatar Da Hare-Hare a Zamfara.

Riƙaƙƙen ɗan bindiga da aka daɗe ana nema, Bello Turji, ya saki mutane 32 da ya yi garkuwa da su, tare da amincewa da dakatar...

Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani Ya Sauya Muƙaman wasu Kwamishinoni guda biyu

Gwamnan, ya aiwatar da wani ƙaramin sauyi a cikin Majalisar Zartaswarsa ta Jihar, inda ya sauya mukaman wasu manyan kwamishinoni guda biyu domin ƙara kuzarin...

Most Popular