Gwamnatin Jihar Katsina ta karɓi wasu mutane su 13 yan asalin jihar, da aka maido daga Birnin Tarayya Abuja da suke yawon Bará
Kwamishinan Raya Karkara Da Walwalar Jama’a Farfesa Abdulhamid Ahmed, shi ne ya karbi mutanen a madadin Gwamnatin Jiha.
A rahoton da Nigerian Post ta samu, Mataimakin Darakta a Sashen Walwala da Jin Dadin Jama’a na Birnin Tarayya ne ya miƙa mutanen ga Kwamishina, a lokacin wani taro da ya gudana a Ma’aikatar Raya Karkara ta jihar Katsina.
Da yake miƙa mutanen, Mataimakin Daraktan ya yabawa Gwamnatin Jihar Katsina a kan kyakkyawar tarba da Gwamnatin Jihar Katsina ta yi wa tawwagar su.
Ya ce an maido mutanen ne a ƙarƙashin shirin tsabtace Birnin Tarayya Abuja daga bárace-bárace da masu bola jari gami da masu kwana a kangaye.
Mataimakin Daraktan ya ce Ministan Abuja ne ya ƙirƙiro shirin, daga nan sai ya buƙaci waɗanda aka maido a kan su nesanta kan su daga halinda suka fita.
A nashi jawabin, Kwamishinan Ma’aikatar Raya Karkara Da Walwalar Jama’a Farfesa Abdulhamid Ahmed, ya yaba wa Sashen Walwalar Jama’a na Birnin Tarayya akan maido da mutanen cikin koshin lafiya.
Farfesa Abdulhamid Ahmed ya tabbatar da cewa ma’aikatar zata kula da mutanen kafin a mika su ga iyalan su nan ba da jimawa ba.
Daga karshe ya bukace su akan su kasance masu halayya ta gari bayan an maida su ga iyalan su.