HomeSashen HausaHanyoyin Da Matasa Ya Kamata Su Bi Domin Gina Rayuwarsu Tun Kafin...

Hanyoyin Da Matasa Ya Kamata Su Bi Domin Gina Rayuwarsu Tun Kafin Tsufa – Inji Ameer Salisu Yaro

-

Da yake ƙarin haske kan shawarwarin, ya ce ‎lokacin samartaka da ƙuruciya ba kawai mataki ne na rayuwa kaɗai ba, mataki ne wanda ake gina Rayuwa da shi. Ya ce Babban kuskure da Matasa ke yi shi ne jiran har sai sun kai wasu shekarun tsufa kafin su fara gina Rayuwar su.

Ya ce hakan, ‎yana ɗaya daga cikin Babban Darasin Rayuwa da ya ɗauka Gameda wasu mashahuran mutane shi ne fara Gina burikan su da manufa tun suna da kananun shekaru. Inda ya bada Misali da Aliko Dangote, shahararren ɗan kasuwar da ya fi kowa a Afrika ya fara Kasuwanci yana dan shekara 20, Mark Zuckerberg mai Facebook ya fara yana shekara 19, Elon musk Wanda ya fi kowa kuɗi Duniya ya fara yana da shekaru 24. akwai misalai na kusa dayawa wanda zan iya kawowa amma na Kawo waɗannan saboda sune suka fi shahara a duniya kuma kusan Kowa ya san su.

‎kamar yadda Nigerian Post ta bibiyi rahoton, ya jaddada cewa, lokacin samartaka da kuruciya lokaci ne da ake koyon duk wani abu da kasan zai iya inganta rayuwar ka. Lokaci ne da ake yin kuskure kuma a gyara, lokaci ne da ake ɗaukar kasada. Lokaci ne na Rashin tsoro saboda a wannan lokacin akwai damar gyarawa.

A cewar sa, ‎tabbas wata rana za su waiwaya su kalli bayan mu sannan mu tuna lokacin kuruciyar su idan sun yi abinda ya da ce, zasu yiwa kansu Godiya idan kuma sun yi akasin haka nadama ce za ta biyo baya wanda ba’a fatan haka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‘Yan Bindigar Da Suka Sace Mutane 3 A Tsakiyar Katsina Sun Nemi Miliyan 600 Kuɗin Fansa

Wasu ’yan bindiga da suka sace wasu ma’aurata da ’yarsu yayin wani hari da suka kai a unguwar Filin Canada da ke Sabuwar Unguwa a...

NSCDC Ta Kama Matashi Ɗauke da Miyagun Ƙwayoyi A Katsina

Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC), reshen jihar Katsina, ta tabbatar da cafke wani Matashi mai shekaru 18 da ake zargi da safarar miyagun...

Most Popular