HomeSashen HausaƳansanda Sun Kama Mutane Biyu Dake Safarar Manyan Makamai Daga Jihar Jigawa...

Ƴansanda Sun Kama Mutane Biyu Dake Safarar Manyan Makamai Daga Jihar Jigawa Zuwa Katsina

-

Rundunar Ƴansandan Jihar Katsina ta yi nasarar chafke masu safarar Makamai daga jihar Jigawa zuwa ƙaramar hukumar Safana ta jihar Katsina, inda aka kama su da miyagun bindugu ƙirar GPMG da harsasai kimanin 1,295.

Da misalin ƙarfe 4:35 na safiyar yau, jami’an rundunar ƴan sandan na ƙaramar hukumar Ingawa da ke sintiri a hanyar Ingawa zuwa ƙauyen Ƙarƙarrku suka tsare wata mota ƙirar Volkswagen Golf mai launin tsanwa da (lambar rijista RSH 528 BY ABJ) ɗauke da wasu makamai da aka ɓoye, inda suka cafke mutum biyu da ake zargi da suke safarar bindigun.

Waɗanda aka kama su ne Abdulsalam Muhammad maj shekara (25) da Aminu Mamman mai shekara (23), dukkan su mazauna kauyen Ɓaure a ƙaramar hukumar Safana.

An same su da manyan makamai da suka haɗa da:

1. Babbar bindiga General Purpose Machine Gun (GPMG) mai lamba Z8826.

2. Harsasai 1,063 na 7.62 x 39mm AK-47.

3. Harsasai 232 na 7.62 x 69mm PKT.

Bincike ya nuna cewa makaman an ɗauko su daga ƙaramar Hadejia, a Jihar Jigawa, za’a kai su ƙaramar hukumar Safana ta jihar Katsina.

A cewar sanarwar, wannan nasara ta nuna jajircewar gwamnati da hukumomin tsaro wajen daƙile hanyoyin da ƴan ta’adda ke samun makamai.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, tuni aka tsunduma bincike domin gano sauran mambobin ƙungiyar, da kuma gano asalin inda wannan ake samo wannan kaya.

Gwamnatin Jihar Katsina ta jinjinawa jami’an rundunar ƴan sanda sakamakon wannan aiki, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da bayar da goyon baya ga hukumomin tsaro a ƙoƙarin su na kawar da aikata miyagun laifuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

NSCDC Ta Cika Hannunta Da Sojin Bogi A Jihar Katsina

Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya Ta (NSCDC) Reshen Jihar Katsina Ta Kama wanda ake zargi da sojan gona amatsayin ma'aikacin hukumar a yan'kin unguwar kwado...

‘Yan Tsagin Wike Sun Gindaya Wa PDP Sabbin Sharudda Kafin Babban Taro

Wasu ƴaƴan jam'iyyar PDP da ake ganin ƴan tsagin Ministan Abuja, Nyesom Wike ne sun gudanar da wani taro a daren jiya Litinin a Abuja,...

Most Popular