Hukumar Tsaro ta NSCDC reshen Jihar Katsina ta samu sabon kwamanda bayan sauyin shugabanci da ya gudana a ranar Litinin, 22 ga watan Satumba, 2025.
A bikin mika mulkin da ya gudana, Commandant Abbas Dan-ile Moriki ya karɓi ragamar shugabancin daga hannun tsohon kwamandan hukumar, Commandant Aminu Datti Ahmad fsf, MADM, FCAI.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, tsohon kwamandan ya godewa Allah Madaukakin Sarki tare da jinjina ga jami’an hukumar bisa goyon baya da haɗin kai da suka bashi a lokacin shugabancinsa. Ya kuma roƙi jami’an da su ci gaba da baiwa sabon kwamandan irin wannan goyon bayan da suka bashi.
A jawabinsa, sabon kwamandan, A.D. Moriki, ya jaddada cewa zai yi aiki bisa manufofin Commandant General na NSCDC, Prof. Ahmed Abubakar Audi mni, OFR, domin tabbatar da tsaro da kuma kariyar manyan kadarorin ƙasa. Ya tabbatar wa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda PhD, CON, da al’ummar jihar cewa zai ɗauki dabarun da suka dace domin ƙarfafa tsaro da kare muhimman wuraren gwamnati da na jama’a.
Sabon kwamandan dai, ya fito ne daga Moriki, ƙaramar hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara. Ya kuma yi karatu a makarantar firamare ta Umaru Danjeka Model Primary School, Moriki da kuma Government Secondary School Koko, Jihar Kebbi. Daga nan ya ci gaba da karatu a Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto, inda ya samu digirin farko a 1995 sannan kuma ya kammala digirin digirgir a fannin tattalin arziki a shekarar 2001.
Commandant Moriki yana da ƙwarewa a fannoni daban-daban na tsaro, inda ya yi aiki a sassa daban-daban na Hukumar NSCDC a jihohi kamar irinsu Kano, Sokoto, Zamfara, Jigawa da Kaduna. Ya kuma halarci horo na musamman kan leƙen asiri da bincike, yaƙi da ta’addanci, tsaro da kariya ga fararen hula, da kuma shirin Disarmament, Demobilization and Reintegration (DDR) a cibiyar horon sojojin Najeriya dake a Jaji, Kaduna.
Shi babban kwararren jami’i ne da ya riƙe manyan mukamai ciki har da: shugaban sashen Antivandal a Kano, sashen gudanarwa a Sokoto, Mataimakin Kwamanda a Zamfara da Jigawa, da kuma Commandant of Administration a hedkwatar NSCDC Zone 2 Kaduna.
Commandant A.D. Moriki yana da aure, da ’ya’ya, kuma yana sha’awar bayar da shawarwari da kuma tafiye-tafiye a sha’anin rayuwar sa.