Hukumar Tsaro ta farin kaya (SSS) ta bayyana cewa za ta ɗauki matakin ladabtarwa a kan jami’an da suka kama kuma suka tsare ’yan jarida biyu na gidan rediyon Jay 101.9 FM a Jos, Jihar Filato.
Premium Times ta rawaito cewa ƴan jaridar, Ruth Marcus da Keshia Jang, sun shiga hannu ne yayin da suke yada rahoto kai tsaye kan rikici tsakanin jami’an SSS da limamai a cocin COCIN, inda ake jana’izar mahaifiyar Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Nantawe Yilwatda.
Shugaban SSS, Adeola Ajayi, ya bayar da umarnin ladabtar da jami’an bayan tabbatar da cewa an saki ’yan jaridar, tare da kiran abin da ya faru “kuskure.”
Lamarin ya jawo cece-kuce daga kungiyoyin kare hakkin ’yan jarida da suka bayyana kamun a matsayin take hakkin faɗar albarkacin baki da kundin tsarin mulki ya tanada.
An rawaito cewa an riga an gano jami’an da ke da hannu a lamarin, kuma hukumar ta fara ɗaukar matakan ladabtarwa a kansu.