Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya sauya manyan shugabannin rundunonin tsaron ƙasar nan domin ƙarfafa tsarin tsaro da inganta tsare-tsaren kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Kamar yadda Nigerian Post ta samu daga Katsina Times, a sabon sauyin da aka sanar daga fadar Shugaban Ƙasa, Janar Olufemi Oluyede ya maye gurbin Janar Christopher Musa a matsayin Shugaban Ma’aikatan Tsaro (Chief of Defence Staff).
Haka nan, Manjo Janar W. Shaibu shi ne sabon Shugaban Sojin Ƙasa, Air Vice Marshal S.K. Aneke ya zama Shugaban Sojin Sama, yayin da Rear Admiral I. Abbas ya karɓi mukamin Shugaban Sojin Ruwa. Sai kuma Manjo Janar E.A.P Undiendeye wanda zai ci gaba da rike mukaminsa na Shugaban Sashen Leken Asirin Tsaro (Chief of Defence Intelligence).
Shugaban Ƙasa Tinubu ya bayyana jin daɗi da godiyarsa ga tsofaffin shugabannin tsaron, musamman Janar Christopher Musa, bisa yadda suka yi aiki da jajircewa da kishin ƙasa a lokacin da suke kan aiki.
Ya kuma bukaci sabbin shugabannin da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, amana da haɗin kai domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a sassan ƙasar nan.
“Na naɗa ku ne bisa amincewa da kwarewarku da kwazonku. Ina sa ran za ku tabbatar da tsaro da haɗin kai a tsakanin rundunonin sojoji,” in ji Shugaban Ƙasa Tinubu.
An bayyana cewa sabbin nadin hafsoshin tsaron sun fara aiki nan take.
