Ɓarawo Ya Sace Motar Ayarin Mataimakin Gwamna A Gidan Gwamnatin Kano
Wani barawon mota ya kutsa cikin Gidan Gwamnatin Kano da sanyin safiyar Litinin ya kuma tsere da wata mota ƙirar Toyota Hilux.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta samu labari cewa barawon motar ya samu damar shiga gidan gwamnatin ta ƙofa ta 4, sannan ya fita da motar da misalin ƙarfe 5 na safe a ranar Litinin ɗin.
Wasu daga cikin ma’aikatan gidan sun ce bayan da aka duba hotunan na’urar CCTV bayan satar, an gano cewa barawon ya fita ta babbar kofar shiga gidan gwamnatin.
Majiyoyi sun shaidawa DAILY NIGERIAN cewa motar na cikin ayarin motocin mataimakin gwamna da ake amfani da su idan zai fita aiki.
A cewar majiyar, tuni aka tsare direban motar mai suna Shafiu Sharp-Sharp donin yi masa tambayoyi.
“An riga an kaddamar da bincike. Ana bincikar direban, yayin da shugaban tsaro na gidan gwamnatin (Chief Security Officer) ke nazarin hotunan CCTV.
“An kuma bai wa jami’an tsaro bayanin motar domin bazama neman ta tare da kama barawon,” in ji majiyar.
DAILY NIGERIAN ta fe ba ta samu jin ta bakin mai magana da yawun gwamna Abba Yusuf, wato Sanusi Dawakin Tofa ba sabida bai amsa kiran wayar wakilin ta ba kuma bai amsa rubutaccen sakon da aka tura masa ba.
