HomeSashen Hausa‎Yansanda Sun Kama Masu Aikata Laifuka Daban-daban, Sun Ceto Mutane 47 da...

‎Yansanda Sun Kama Masu Aikata Laifuka Daban-daban, Sun Ceto Mutane 47 da Aka Yi Garkuwa da Su a Jihar Katsina

-

Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Katsina ta bayyana cewa ta samu nasarori masu yawa a yakin da take yaki da laifuka, ciki har da kama mutanen da ake zargi da aikata manyan laifuka, da kuma kubutar da mutane 47 da aka yi garkuwa da su tare da 39 da aka ƙwato daga hannun masu safarar mutane.

‎Wannan bayani ya fito ne daga bakin Kakakin Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Katsina, DSP Aliyu Abubakar Sadiq, yayin da yake ganawa da Manema Labarai a hedkwatar rundunar ranar Talata 11 ga watan Nuwamba 2025 a Katsina, inda ya bayyana cikakken rahoton nasarorin da suka samu cikin makonnin baya-bayan nan.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, ‎a cewar rundunar, an kama wadannan mutanen ne bayan binciken rahotanni 120 da suka shafi fashi da makami, kisa, fyade, safarar miyagun kwayoyi, da garkuwa da mutane.

 

‎Daga cikin jerin mutanen da aka kama akwai:

‎Mutane 18 da ake zargi da fashi da makami, ‎Mutane 28 da laifukan kisa, ‎Mutane 5 da yunkurin kisa, ‎Mutane 20 da laifin fyade, ‎da kuma Mutane 28 kuma da laifin safarar miyagun kwayoyi.

‎Haka kuma, an gurfanar da rahotanni 97 gaban kotu, yayin da 22 ake ci gaba da bincike.

‎A yayin taron, an nuna wasu abubuwan da rundunar ta kwato, ciki har da bindigar AK-47 guda daya, bindiga ta gida, harsasai 183, manyan motocci, babura, da dabbobin da aka sace fiye da 200. An kuma gano miyagun kwayoyi irin su Tramadol, Exol, Fentalin, da wiwi, da kuma wayoyin lantarki da aka lalata.

‎DSP Sadiq ya tabbatar da cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da tsaro a dukkan sassan jihar, yana mai cewa:

‎“Ko da yake an samu nasarori masu yawa, amma har yanzu akwai sauran aiki. Rundunar za ta ninka kokarinta don tabbatar da cewa Jihar Katsina ta zama wuri mafi aminci.”

‎Ya kuma gode wa Sufeton ‘Yan Sanda na Kasa, IGP Kayode Egbetokun, da Gwamnatin Jihar Katsina bisa goyon bayan da suke baiwa rundunar wajen yaki da laifuka.

‎Sai kuma ya gargadi jama’a kan yada labaran karya (fake news), yana mai cewa hakan na iya haddasa rudani da rage amincewar jama’a ga hukumomin tsaro.

‎A karshe, rundunar ta roki al’umma da su ci gaba da ba da bayanai masu inganci da za su taimaka wajen hana aikata laifuka, tare da tabbatar musu cewa duk wani rahoto da aka bayar za a bibiyeshi cikin sirri da kariya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Nijeriya Ta Musanta Zargin Leken Asiri Kan Jirginta Da Ke Burkina-Faso

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta karyata jita-jitar da ke cewa jirginta kirar C-130 da ya sauka ba tare da shiri ba a Bobo-Dioulasso,...

Duniya Za Ta Fuskanci Ƙalubale, Idan Najeriya Ta Wargaje– Inji Sanata Kashim Shettima

Mataimakin Shugaban Ƙasa a Najeriya, Kashim Shettima ya ce gwamnatin Tinubu ba za ta taɓa bari Najeriya ta ruguje a hannunta ba, komai rintsi.   Kamar yadda...

Most Popular