Haɗakar Jami’an Tsaron Sa-kai na Ƙasa (CJTF) ta ci alwashin karar da ƴanbindiga da ke addabar wasu sassa na Arewacin Nijeriya a cikin shekara ɗaya take.
Farfesa Kailani Muhammad, Shugaban CJTF na Ƙasa ne ya baiyana hakan yayin da Charles Omini, Jakadan Musamman na Kungiyar Kare Hakkin Dan’adam na Afrika ta Yamma ya mika masa takardar zama ɗan hadaddiyar kungiyar jami’an sa-kai ta Afirka ta Yamma (JTF) a Abuja a ranar Asabar.
A cewar Muhammad, da Gwamnatin Tarayya ta ba da ƙarfi tare da tallafa wa CJTF kayan aiki,’ da suka dace to za su murƙushe ’yan bindiga cikin shekara guda.
Ya yi kira ga gwamnati da ta ba Civilian JTF goyon bayan da ya dace domin su nuna abin da za su iya yi.
