HomeSashen HausaRundunar Sojin Najeriya Sun Kama Wani Fitaccen Mai Garkuwa Da Mutane A...

Rundunar Sojin Najeriya Sun Kama Wani Fitaccen Mai Garkuwa Da Mutane A Taraba

-

Rundunar ta kama mai suna Alhaji Abubakar Bawa a Kudancin Taraba.

 

Ana zargin Bawa yana da alaƙa da wani shahararren mai garkuwa da mutane, Umar Musa, wanda aka kama a kwanakin baya.

 

Binciken ya nuna suna cikin wata babbar ƙungiyar laifuka da ke da alhakin garkuwa da mutane da kai hare-hare a yankin.

 

Kwamandan Brigade ta 6 ya yaba wa sojoji bisa nasarar, yana mai cewa Operation Zafin Wuta na yunƙuri wajen lalata ƙungiyoyin dake aikata laifuka, kuma za su ci gaba da aiki ba tare da sassauci ba.

 

Sojoji suna cigaba da bincike kan sauran abokan hulɗar wanda aka kama, kuma Rundunar Soji tayi kira ga jama’a da su riƙa bayar da bayanai. Bawa yana tsare yanzu kuma ana ci gaba da tambayarsa.

 

Daga Aliyu Adamu Tsiga

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Dalilan Da Ya Sa Na Bar APC Na Koma ADC– Inji Wada Protocol

‎Tsohon hadimin tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, Alhaji Mustapha Abdu Saulawa, wanda aka fi sani da Wada Protocol, ya bayyana dalilin da...

Yaron Shago Ya Hallaka Ubangidansa da Almakashi a Gombe, Kwanaki Kadan Da Aurensa

Jihar Gombe ta shiga alhini biyo bayan wani mummunan lamari da ya faru a unguwar Bolari, cikin birnin Gombe, inda wani yaron shago ya kashe...

Most Popular