HomeSashen HausaMace Mai Juna Biyu Ta Rasa Ranta Bayan Ma’aikaci Ya Ki Karɓar...

Mace Mai Juna Biyu Ta Rasa Ranta Bayan Ma’aikaci Ya Ki Karɓar Transfer Don Biyan Kudin Iskar Numfashi A Asibitin Turai Katsina

-

Mace Mai Juna Biyu Ta Rasa Ranta Bayan Ma’aikaci Ya Ki Karɓar Transfer Don Biyan Kudin Iskar Numfashi A Asibitin Turai Katsina

Wata mata mai juna biyu, Aisha Najamu, ta rasu a Asibitin Turai Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina bayan ma’aikatan asibitin sun ki karɓar kudin oxygen ta hanyar tura kudi (transfer), sun dage cewa sai an biya kudi a hannun (cash) kafin a ba ta agajin gaggawa.

Wadanda suka gani da idonsu sun shaida ma Katsina Times cewa matar tazo asibitin cikin mawuyacin hali tana bukatar iskar numfashi da gaggawa, amma mai karɓar kudi ya ki bada rasidi ko aiwatar da biyan kudin saboda bata da kudi a hannu. Ma’aikacin ya dage kan cewa dokar asibitin ta haramta karɓar transfer.

Wani mutum da ya shiga tsakani ya ce ya roƙi ma’aikacin da ya karɓi transfer domin a ceto rayuwar matar, amma ma’aikacin ya nace kan cewa ba zai karya dokar asibiti ba. Mutumin ya ce har ya yi masa tayin ɗaukar dukkan bashin da kuma ƙarin kuɗi,ta hanyar yi masa transfer saboda shima bashi da Kash, karshe dai har ya miƙa masa dala $100 don ya karɓa ya ceto matar, amma ma’aikacin ya ƙi yarda.

Mutumin ya bayyana cewa lamarin ya faru kusan ƙarfe 11:30 na daren jiya talata wayewar garin yau Laraba 3 ga watan Disamba 2025.

Yayin da ba inda za a iya samun kudi a hannun. Ya ce Aisha na kuka tana roƙon a taimaka mata, amma kafin a samu mafita ta rasu tana neman agaji.

Da muka tuntubi hukumar Asibitin Turai Umaru Musa Yar’adua, sun ce ba su samu korafi daga jama’a ba sai na kungiyar kare hakkin dan Adam ta IHRAAC. Wakilin manajan asibitin, Aminu Ibrahim Kofar Bai, ya jajanta ya kuma tabbatar da cewa za su ziyarci iyalan mamaciyar tare da binciken duk ma’aikacin da ya yi sakaci.

Asibitin ya kare kansa da cewa tsarin gwamnatin Katsina ta TSA ne ya hana karɓar transfer, kuma ba su da POS da za a iya amfani da shi. Sun kuma koka da karancin iskar oxygen, inda suka ce daga Daura kawai suke iya samo shi.

Shugaban bangaren Pharmacy, Perm Usman Salisu Wada, ya ce ma’aikacin da abin ya shafa “ya yi tsauri wajen bin doka” saboda tsoron zargi. Ya ce wasu marasa lafiya da ake taimakawa ma sukan ki biyan kudin bayan sun warke.

A wani lamari mai kama da haka, wani magidanci, Rabi’u Yakubu, ya zargi ma’aikatan jinya da sakaci wajen kara wa matarsa Khadijah Rabi’u jini. Ya ce an gaza saka mata leda ta biyu na jini tsawon sa’o’i har sai da jinin ya lalace.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa irin wadannan matsaloli sun yawaita a asibitocin Katsina saboda karancin ma’aikata. Wani ma’aikaci ya ce fiye da kashi biyu bisa uku na ma’aikatan asibitin Turai “casual” ne masu karbar albashin dubu goma kacal.

Rahotanni kan sakaci, rashin kulawa ga marasa lafiya, da tsaurin bin dokoki suna ci gaba da janyo fushi da damuwar jama’a game da kiwon lafiya a jihar Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Tsofaffin Ma’aikatan FRCN, Sun Shirya Jagorantar Zanga-zanga Zígídír, Kan Ƙin Biyansu Haƙƙinsu A Najeriya

A wani rahoto da Nigerian Post ta samu daga Aminiya, an tabbatar da cewa, tsofaffin ma’aikatan (FRCN) Federal Radio Corporation of Nigeria (FRCN) sun ce...

Hadiza Gabon Na Shirin Barin Kaduna Zuwa Kano Da Shirin Talk Show

Daya daga cikin makusantar tsohuwar Jarumar Kanywood Hadiza Gabon, ya tabbatar wa Jaridar ALFIJIR NEWS, wanda a yanzu jarumar ta fara tinanin dauke zauren Shirin...

Most Popular