Majalisar Kansiloli ta Ƙaramar Hukumar Katsina ta gudanar da zamanta na biyu tun bayan kammala sabunta ginin majalisar, a wani mataki da ke nuni da sabon shiri wajen ƙarfafa tafiyar da al’amuran Mazaɓun ƙaramar hukumar, da sauraron muradun jama’a kai tsaye.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, zaman majalisar ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar Dokokin Ƙaramar Hukumar Katsina, Hon. Ishaq Tasiu Modoji, inda kansiloli daga mazabu daban-daban suka hallarci zaman domin gabatar da ƙudurori da koke-koken da suka shafi muhimman bukatun al’ummar da suke wakilta.
A yayin zaman, kansilan Mazabar Arewa A. ya gabatar da ƙudurin cike tafkin Marna, samar da hanyoyin ruwa, tare da buƙatar saka fitilu masu amfani da hasken rana a wasu unguwanni domin inganta tsaro da walwalar jama’a.
Haka kuma, Kansilan Mazabar Yamma II, ya nemi a gina magudanan ruwa a Unguwar Ceceniya, tare da cike tafkin Tsatstsagau domin shawo kan matsalar ambaliya da lalacewar muhalli.
Kazalika, a Mazabar Kudu II, kansilan ya gabatar da ƙudurorin da suka haɗa da cike tafkin Asabe, gina sabuwar makaranta, da kuma gyaran makarantar Islamiyya da ke Yansiliyu. Haka kuma, ya buƙaci a mayar da makarantar Kofar Kaura zuwa makarantar bene (Isah Kaita (B) Primary School), tare da samar da fitilu masu amfani da hasken rana guda 300 a fadin mazabar.
Shi ma Kansilan Mazabar Shinkafi A, ya mayar da hankali kan buƙatar gina hanyar ruwa daga Sabon Garin wayau zuwa Shinkafi, tare da gyaran kasuwar Danabaso domin bunƙasa harkokin kasuwanci.
A Mazabar Kudu III, an gabatar da ƙorafi kan buƙatar gina hanyoyin ruwa daga Yankaji zuwa Ƙoramar Nayalli, da kuma unguwar Abatuwa zuwa Janbango.
Kansilan Mazabar Kangiwa ya gabatar da ƙudurin gina hanyar ruwa a Tudun Baras, tare da buƙatar samar da fitilun masu amfani da hasken rana guda 400 a yankin Hayin Gada.
Daga Mazabar Gabas II kuwa, an nemi a mayar da makarantar Barda Primary School zuwa makarantar bene, tare da gyaran makarantar Kidis domin ɗaukaka ta zuwa makarantar sakandare.
Kansilan Mazabar Shinkafi B, ya gabatar da jerin ƙudurori da suka haɗa da gina hanyar ruwa daga layin Kanyar ’Yayan Mage zuwa bayan IBS, gina rijiyar burtsatse mai tankuna huɗu da ke aiki da hasken rana a Bumbum, gyaran makarantu a Garin Bakuru da kuma cike tafkin Modoji da ke kusa da makabarta.
A Mazabar Wakilin Gabas, kansilan yankin ya nemi a gina makarantar Islamiyya, tare da gina rijiyoyin burtsatse masu amfani da wutar lantarki guda biyu a Unguwar Iyatanchi.
Kansilan Mazabar Arewa B, ya gabatar da koken al’ummarsa, inda ya buƙaci gina magudanan ruwa daga Katoge zuwa Lambun Danlawan, da kuma daga Kofar Soro Quarters zuwa New Map.
Haka kuma, kansilan Mazabar Yamma I ya gabatar da ƙudurin gina hanyar ruwa a Unguwar Sabon Gida.
Masu lura da al’amuran ƙananan hukumomi na ganin wannan zama a matsayin wani muhimmin mataki na ƙarfafa dimokuraɗiyya a matakin ƙasa, inda aka bai wa muradun jama’a muhimmanci, tare da fatan ƙudurorin da aka gabatar za su samu aiwatarwa domin inganta rayuwar al’ummar Ƙaramar Hukumar Katsina.
