HomeLabaraiTsohon gwamnan Sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya koma jam’iyar APC

Tsohon gwamnan Sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya koma jam’iyar APC

-

Bafarawa da magoya bayansa sun bayyana komawa jam’iyar APC a babban xakin taro na gidansa dake jihar Sakkwato a ranar Laraba.

 

Tsohon Gwamnan ya ce magoya bayansa huldarsu da jam’iyar APC za ta kasance ne a tsakanin shugaban qungiyar magoya bayansa Farfesa Hamza Maishanu da jam’iya.

 

“Siyasar da nake faxin na bari ita ce ban shiga takarar kujera kowace iri, amma ina son magoya bayana su samu nasara.”

 

“Akwai ‘yan siyasar kwangila da neman muqami dana maula duk in da ta juya can za su je, a lokacin da nake gwamna ban gane irin wannan halin sai da na sauka.”

 

Komawar Bafarawa a APC bai zo da mamaki ba ganin yadda hulxa ta qullu tsakaninsa da jam’iyar APC a jiha musamman yadda yake yabon Gwamnan Sakkwato Ahmad Aliyu, da yawan mutane suna zaton zai shiga APC kamar yadda ya faru a yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Katsina Police Arrest Suspected Kidnapper, Bandit Informant in Matazu

The Katsina State Police Command has arrested a 45-year-old man, identified as Surajo Isyaku, over alleged involvement in kidnapping, cattle rustling and providing information to...

Dangote Refinery Reduces Aviation Fuel Price by N100 Per Litre

Dangote Refinery has announced a reduction in the price of Jet A1 aviation fuel from N1,750 to N1,650 per litre, in a move aimed at...

Most Popular