Shugaban Hukumar NMDPRA, Injiniya Farouk Ahmed, ya ajiye aikinsa, lamarin da ya buɗe sabon babi a jagorancin hukumomin da ke kula da harkokin man fetur a ƙasar.
Farouk Ahmed na daga cikin shugabannin da aka naɗa a shekarar 2021, bayan kafuwar NMDPRA karkashin Dokar Petroleum Industry Act (PIA), wadda ta kawo sauye-sauye a tsarin kula da albarkatun man fetur da gas.
Murabus ɗinsa na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tura sunayen sababbin shugabanni gaban Majalisar Dattawa domin tantancewa da amincewa, a ƙoƙarin da gwamnatin ke yi na ƙarfafa shugabanci da tabbatar da daidaito a muhimmin sashen makamashi.
A cewar Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara ta Musamman kan Bayanai da Dabaru, Bayo Onanuga, murabus ɗin Farouk Ahmed da na shugaban NUPRC Gbenga Komolafe ne ya ba Shugaban Ƙasa damar miƙa sunayen sababbin ƙwararru domin ci gaba da aiwatar da manufofin PIA.
Masu lura da harkokin makamashi na ganin wannan sauyi a matsayin wani muhimmin mataki da zai iya tasiri kai tsaye kan harkokin tace mai, rarrabawa da farashin man fetur a Najeriya.
