Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina, karkashin jagorancin Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Bello Shehu, MNIM, ta shirya wani Maci na wayar da kan jama’anta kan Yaki da Kungiyoyin Asiri da Sauran Munanan Ayyuka domin fadakar da al’umma kan illar aikata laifuka ga rayuwar jama’a da kuma karfafa hadin gwiwa tsakanin ‘yan sanda da al’umma, domin samun Jihar Katsina mai tsaro, musamman a karshen shekara.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, Tafiyar wadda aka gudanar a cikin birnin Katsina kan titin Sarki Abdulrahman Way, GRA, Katsina, ta samu halartar jami’an rundunar ‘yan sanda da kuma masu ruwa da tsaki.
Kwamishina, CP Bello Shehu wanda shine ya jagoranci tafiyar, ya jaddada kudurin rundunar na yakar laifuka da tabbatar da tsaron al’ummomin jihar.
Ya bayyana cewa laifuka na da mummunan tasiri ga ci gaba, tare da yin alkawarin cewa rundunar za ta ci gaba da goyon bayan duk wasu shirye-shiryen da ke inganta zaman lafiya da tsaro. Ya kuma bukaci al’umma da su yi hadin gwiwa da ‘yan sanda ta hanyar kai rahoton duk wani abu da ake zargi, musamman a wannan lokaci na karshen shekara.
Shirin POCACOV na inganta gaskiya, rikon amana da hadin gwiwa tsakanin ‘yan sanda da al’umma. Rundunar ta bukaci jama’a da su shiga sahun gaba wajen yaki da laifuka.
Bayanin na kunshe ne a cikin sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar.
