HomeSashen HausaNDLEA ta kama mutane 424 ɗauke da miyagun ƙwayoyi a Katsina

NDLEA ta kama mutane 424 ɗauke da miyagun ƙwayoyi a Katsina

-

A ƙoƙarin da hukumar NDLEA take yi na daƙile sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a jihar Katsina, ta kama mutane 424 ɗauke da miyagun ƙwayoyi a sassan jihar.

Kwamandan hukumar a Katsina Sama’ila Ɗan Malam, shi ne ya sanar da haka lokacin da yake ganawa da Manema Labarai ranar Alhamis 26 ga watan Yuni 2025 a hedkwatar hukumar.

Ya ce waɗannan mutane da aka kama a cikin watanni Shida, an gurfanar da mutane 44 a kotu daga cikin mutane 34, inda kotu ta hukunta su, wanda ya zuwa yanzu suna can tsare a gidajen gyaran hali.

Haka kuma mutane 194 cikin waɗanda hukumar ta kama, sun kammala horo na gyaran halinka da aka saba gudanar wa na tsawon mako ɗaya.

Kazalika, Kwamandan ya bayyana cewar, akwai mutane 24 da suma aka basu horo na gyara halin ka na tsawon watanni Uku zuwa Shida, daga cikin su mutane 16 sun kammala ɗaukan horon har sun koma wajen iyalan su.

Ya ce hukumar a Katsina ta gudanar da tarurruka na faɗakarwa a kan illar ta’ammali da miyagun ƙwayoyi har sau 96.

Mutane 21,565 suka halarci faɗakarwar da hukumar ta gudanar a wurare daban-daban a faɗin jihar.

Tunda farko, Kwamandan Sama’ila ya yaba wa gwamnatin jihar da sauran jami’an tsaro da sarakuna, ƙungiyoyin sa kai da sauran al’umma wajen ƙokarin da hukumar keyi na tsarkake jihar daga ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Har Yanzu Ba Mu Ayyana Wanda Ya Lashe Zaɓen Takarar Kujerar Majalisar Anambra Ba- INEC

Anambra, 16 ga Agusta 2025 – Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta tabbatar da cewa tana ci gaba da tattara sakamakon zaɓen...

Jami’an Tsaro Sun Kama Manyan Shugabannin Kungiyar Ansaru

Mai Ba wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro na Ƙasa (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun samu gagarumar nasara ta hanyar...

Most Popular