HomeLabaraiDalilan da su ka sa Ganduje ya yi murabus na shugabancin jam'iyyar...

Dalilan da su ka sa Ganduje ya yi murabus na shugabancin jam’iyyar APC

-

Dalilan da su ka sa Ganduje ya yi murabus na shugabancin jam’iyyar APC

A cikin wani mataki da ya ba da mamaki, Abdullahi Umar Ganduje, Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, ya yi murabus daga mukaminsa nan take.

Ganduje, tsohon Gwamnan Jihar Kano, ya bayyana dalilin neman lafiya a matsayin abin da ya sa ya yanke shawarar sauka daga kujerar, yana mai cewa yana buƙatar mayar da hankali kan lafiyarsa.

Jaridar Premium Times ta rawaito cewa duk da cewa takardai murabus din na sa ta danganta saukarsa da batun lafiya, majiyoyi da ke da masaniya da al’amarin sun nuna cewa, akwai yiwuwar rikici na siyasa a cikin jam’iyyar, wanda hakan ya taka rawa wajen yanke shawarar da ya ɗauka.

An yi hasashen dangantakar saukarsa na ɗaya daga cikin wasu zarge-zargen almundahana da suka shafi harkar kuɗi, inda wasu mambobin jam’iyyar suka bayyana rashin jin daɗinsu kan yawan bukatun kuɗi fiye da kima da ofishinsa ke kakaba wa ya’yan jam’iyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Katsina Police Arrest Suspected Kidnapper, Bandit Informant in Matazu

The Katsina State Police Command has arrested a 45-year-old man, identified as Surajo Isyaku, over alleged involvement in kidnapping, cattle rustling and providing information to...

Dangote Refinery Reduces Aviation Fuel Price by N100 Per Litre

Dangote Refinery has announced a reduction in the price of Jet A1 aviation fuel from N1,750 to N1,650 per litre, in a move aimed at...

Most Popular