A cikin wata sanarwa da rundunar Operation Fansan Yamma ta fitar, ta ce an kai harin ne bayan samun sahihan bayanan sirri da suka nuna cewa wasu shugabannin ƴan ta’adda sun hallara a yankin. Rundunar ta bayyana cewa harin ya lalata maɓoyar ƴan bindigar tare da kashe da dama daga cikinsu.
Sai dai mazauna yankin da wasu ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama sun bayyana cewa fararen hula da dama sun rasa rayukansu a harin. Rahotanni daga yankin sun nuna cewa harin ya afku ne kusa da kasuwa da gidajen jama’a, abin da ya haddasa asarar rayuka masu yawa ciki har da mata da yara.
Rahoton da Nigerian Post, ta samu daga DCL Hausa, ya bayyana cewa wani harin sama da rundunar sojin saman Najeriya ta kai a jihar Zamfara ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 100 a yankin Tumfa da ke ƙaramar hukumar Zurmi/Shinkafi.
Wasu majiyoyi sun ce adadin waɗanda suka mutu ya haura 100, yayin da aka samu mutane da dama da suka jikkata sakamakon harin.
Kungiyar Amnesty International ta buƙaci a gudanar da cikakken bincike domin gano hakikanin abin da ya faru tare da tabbatar da adalci ga waɗanda lamarin ya shafa.
Sai dai rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin cewa an kai hari kan fararen hula da gangan, tana mai cewa farmakin ya ta’allaka ne kan maɓoyar ƴan ta’adda bayan samun ingantattun bayanan sirri.
Lamarin ya sake tayar da muhawara kan yadda hare-haren sama ke haddasa asarar rayukan fararen hula a yankunan da ake fama da matsalar tsaro a Najeriya.
