Tuesday, June 16, 2026
HomeLabaraiAn Kama Wasu Matasa Bisa Wani Aure Da Aka Daura Kan Sadakin...

An Kama Wasu Matasa Bisa Wani Aure Da Aka Daura Kan Sadakin N3,000 a Bauchi

Rahotanni daga Jihar Bauchi sun nuna cewa jami’an tsaro sun kama wasu matasa bayan wani aure da aka daura wa wasu matasa a kan sadakin Naira 3,000 ya jawo ce-ce-ku-ce a gari.

An ce an kama angon, amaryar da wasu abokansu bayan umarnin da gwamnatin jihar ta bayar na gudanar da bincike kan lamarin.

Shugaban ƙungiyar ‘yan sintiri ta jihar ya bayyana cewa an shafe kwanaki ana neman matasan kafin daga bisani aka cafke su.

Lamarin dai ya haddasa muhawara a tsakanin al’umma, inda mutane ke bayyana mabambantan ra’ayoyi kan batun.

Me ra’ayinku kan wannan lamari?

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments