Jerin basarori 12 da Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kafa a shugabancin jam’iyyar APC na ƙasa da babu shugabanta da ya taɓa kafawa a cikin shekara 12 da kafuwarta.
1- A ƙarƙashin jagorancin Ganduje ne Gwamnoni biyu suka shiga Jam’iyyar APC, Gwamna Sherrif Oborevwori na jihar Delta.
2-Gwamnan Akwa Ibom ya koma APC Umo Eno
3- Tsohon Gwamnan Delta, kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa Ifeanyi Okowa.
4– APC ta samu ƙarin Sanatoci 10 a ƙarƙashin shugabancin Ganduje
5 – A majalisar Wakilai ta tarayya kuma, daga ƴan majalisa 175 da aka rantsar a 2023, ƴan majalisa 32 sun shiga APC daga jam’iyyun adawa daban-daban.
6 – APC ta kwato Jihar Edo daga hannun PDP a karkashin jagorancin Ganduje.
7–Ya tabbatar da jihar Kogi ta ci gaba da zama ƙarƙashin jam’iyyar APC duk da adawar da ta fuskanta a zaɓen gwamna jihar.
8 – APC ta yi nasara a zaɓen gwamnan Jihar Ondo
9–Jihar ita ma ta cigaba da zama ƙarkashin ikon APC.
10– Ganduje ya sasanta taƙaddamar da ya kusa cinye jam’iyyar APC a jihar Ondo, tsakanin gwamna marigayi Akeredolu da mataimakinsa Luck.
11– Ƙarƙashin Ganduje, an kafa ofisoshin APC a mazaɓu 8,813 a faɗin Najeriya
12– Ƙirkiro da yin rijistan zama ɗan jam’iyyar ta hanyar fasahar zamani