Babban uba ga PCRC Alhaji Sabo Musa, ya jagoranci ƙaddamar da sabbin jami’ai da za su rinƙa ba ‘Yandanda bayanai a ƙananan hukumomi 8, da suka haɗa da Dandume, ƙaramar hukumar Katsina, Dutsinma, da sauran su.
Majiyar ta samu cewa, an kaddamar da su ne domin bada bayanai a kowacce Unguwa a jihar, da kuma kashe duk wasu fitintinu a cikin unguwanni, idan abin kuma ya fi karfinsu su kai rahota ga manyan jami’an tsaro.
Lokacin da ake ƙaddamar da su, masu ruwa da tsaki na ɓangaren tsaro a jihar Katsina sun ziyarci taron, domin haɗa kai da duk wani sashe na jami’an tsaro a jihar.
A wani rahoto da Nigerian Post ta samu, lokacin da ake ƙaddamar da shuwagabannin jami’an a jihar, Alhaji Sabo Musa, shi ne a ƙaddamar da su a ranar Lahadi da ta gaba a birnin Katsina.
An kuma ja kunnen su da su kasance ma su gaskiya da amana ba tare da sun ci amanar yankunan su ba ko kuma karya dokar da ta shafi ƙasa, an ce ma su, ya zama wajibi su bi doka da oda kar su kasance sun tauye haƙƙin wasu.