HomeSashen HausaGwamnatin Katsina Za Ta Farfaɗo da noman Auduga da gina Cibiyar Sarrafa...

Gwamnatin Katsina Za Ta Farfaɗo da noman Auduga da gina Cibiyar Sarrafa Nama

-

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ƙuduri aniyar farfaɗo da noman Auduga da kuma kafa babbar cibiyar sarrafa Nama a jihar, domin zuba jari daga masu zaman kansu da kuma samar da aikin yi a jihar.

Ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi baƙuncin Darakta Janar na Hukumar Binciken Kimiyyar Halitta ta Ƙasa (NBRDA), Farfesa Abdullahi Mustapha, wanda ya zo don ƙulla haɗin gwiwa tsakanin hukumar da kamfanin Dar Al-Halal Animal Farm.

Kamar yadda wakiliyar Nigerian Post ta bibiyi batutuwan Sadiya Sani Sadiq, an shirya haɗin gwiwar ne don gina katafaren matattarar Nama da za ta sanya Najeriya ta shiga sahun ƙasashen da ke fitar da Nama zuwa waje, tare da samar da dubban ayyukan yi a Katsina.

Gwamna Radda ya ce, Manoma da dama sun daina noman Auduga saboda rashin ingantattun iri, inda ya jaddada cewa suna shirin kawo sabbin iri da tallafi don su dawo da darajar Noma.

Ya ƙara da cewa, Noma ne tushen ci gaban tattalin arzikin jihar, kuma gwamnatinsa za ta ci gaba da raba taki da kayan aiki domin tallafa wa Manoma.

Shi ma, Farfesa Mustapha ya jinjina wa Gwamna Radda, bi sa yadda ya ke ba da muhimmanci ga harakokin Noma da Kimiyya, inda ya ce wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen bunƙasa Abinci, rage talauci da haɓɓaka cigaban jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Gwamnatin Kano ta biya wa fursunoni 58 sun zana jarabawar NECO ta 2025

A wani muhimmin mataki na gyaran hali da rayuwar ɗaurarru, fursunoni 58 a jihar Kano ne su ka zana jarabawar kammala makarantar sakandire ta kasa,...

Ko Seyi Tinubu Ne Ya Zama Shugaban INEC, APC Za Ta Sha Kaye a 2027 -inji Dalung

Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya bayyana cewa jam’iyyar APC da shugaban ƙasa Bola Tinubu ba za su tsira ba a zaben 2027,...

Most Popular