HomeSashen HausaShugaban Ƙasar Gambiya Adama Barrow, Ya Kai Ziyarar Ta’aziyyar Rasuwar Tsohon Shugaban...

Shugaban Ƙasar Gambiya Adama Barrow, Ya Kai Ziyarar Ta’aziyyar Rasuwar Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari A Katsina

-

Shugaban ƙasar Jamhuriyar Gambiya, Mista Adama Barrow, tare da uwargidansa, Hajiya Fatoumatta Bah Barrow, da tawagar Gwamnati, sun kai ziyarar ta’aziyya a garin Daura dake Jihar Katsina, dangane da rasuwar tsohon Shugaban ƙasar Najeriya, marigayi Muhammadu Buhari, GCFR.

An tarbi Shugaba Barrow da tawagarsa a Filin Jirgin Sama na Malam Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina, inda Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Garba Faskari, ya wakilci Gwamnan Jihar, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, wanda suka karɓarsu hannu biyu.

Nigerian Post ta samu cewa, Daraktan Yaɗa Labarai na sakataren gwamnatin jihar Katsina, Alh Abdullahi Aliyu Yar’adua, shi ne ya fitar da takardar hakan ɗauke da sa-hannun sa, sannan ya kuma rabawa Manema Labarai.

Bayan isowarsu, shugaban ƙasar Gambiya da tawagarsa sun nufi gidan marigayin tsohon shugaban ƙasa a Daura, inda suka yi ta’aziyya da nuna alhini, tare da kai ziyara zuwa makwancinsa domin yin addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta masa, ya karɓi ayyukan alherinsa, ya sanya shi cikin rahamarSa, kuma ya ba iyalinsa da al’ummar Najeriya haƙurin jure wannan babban rashi.

Shugaba Barrow ya bayyana marigayi Buhari a matsayin ɗaya daga cikin fitattun shugabannin Afirka da suka tsaya tsayin daka wajen kafa tsarin dimokuraɗiyya da gina ingantacciyar ƙasa. Ya ce Najeriya da ma nahiyar Afirka sun yi rashi mai girma, sannan ya bayyana marigayin a matsayin uba, aboki, da jigo wajen samar da zaman lafiya da ci gaba a yankin yammacin Afirka.

A cewar sa, ƙasar Gambiya ta rasa Babban Uba Mai hangen nesa da kishin al’ummar Afirka baki ɗaya.

A gidan marigayin, uwargidan tsohon shugaban ƙasa, Hajiya A’isha Buhari, da ɗansa Yusuf Buhari, sun karɓi shugaban Gambiya da tawagarsa, inda suka nuna godiya bisa irin ƙoƙarin da suka yi na zuwa da kansu domin jajantawa da nuna ƙauna.

Yusuf Buhari, wanda ya yi jawabi a madadin iyalin marigayin, ya gode wa Shugaba Barrow da tawagarsa bisa wannan ziyara ta girmamawa da alhini, yana mai cewa wannan lamari ya ƙara nuna zumunci da haɗin kai tsakanin ƙasashen Gambiya da Najeriya.

Shi ma da yake jawabi a madadin Gwamnan Jihar Katsina, Sakataren Gwamnati, Abdullahi Garba Faskari, ya yaba da wannan ziyara, yana mai cewa Katsina da Najeriya baki ɗaya na godiya bisa wannan ɗabi’ar ɗan’uwa da ɗan’Adam. Ya kuma yi addu’ar Allah ya mayar da su gida lafiya.

Shugaba Adama Barrow da tawagarsa sun bar Jihar Katsina da yammacin Jumu’a, inda wasu mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar suka rako su zuwa filin jirgi domin ban kwana.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Ɓarawo Ya Sace Motar Ayarin Mataimakin Gwamna A Gidan Gwamnatin Kano

Ɓarawo Ya Sace Motar Ayarin Mataimakin Gwamna A Gidan Gwamnatin Kano Wani barawon mota ya kutsa cikin Gidan Gwamnatin Kano da sanyin safiyar Litinin ya kuma...

‎Yansanda Sun Kama Masu Aikata Laifuka Daban-daban, Sun Ceto Mutane 47 da Aka Yi Garkuwa da Su a Jihar Katsina

Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Katsina ta bayyana cewa ta samu nasarori masu yawa a yakin da take yaki da laifuka, ciki har da kama mutanen...

Most Popular