Gwamnatin Jihar Katsina ta gudanar da horo na kwana ɗaya ga Malaman Gona 756 da kuma Jami’an Cigaban Al’umma (CDO’s) a fannoni na dabarun kiwon dabbobi na zamani da kuma buƙatar shawarwari na musamman don samun nasarar kiwo a jihar. Taron ya gudana ne a dakin taro na Sakatariyar Jihar Katsina a ranar Litinin 18 ga watan Agusta, 2025.
A yayin taron, Mai Ba Gwamna Shawara kan Harkokin Kiwon Dabbobi da Gandun Daji, Hon. Yusuf Suleiman Jibia, ya bayyana cewa manufar shirin ita ce wayar da kan mahalarta kan hanyoyin zamani da ake amfani da su a fannin kiwon dabbobi a duniya. Ya ce gwamnatin Dikko Radda ta himmatu wajen inganta kiwon dabbobi, ciki har da rarraba ingantattun awaki ga mata da al’ummomi, aiwatar da rigakafin dabbobi lokaci zuwa lokaci, da kuma gina wuraren kiwo na zamani.
Shugaban Hukumar Bunƙasa Ayyukan Gona ta Jihar Katsina (KTARDA), Alhaji Abubakar Dabo, ya bayyana cewa kasancewar Gwamna Dikko Radda ƙwararre ne a fannin noma ya zama abin alfahari da kuma ci gaba ga jihar. Ya ce kafin zuwan Radda, jihar Katsina ba ta da Malaman Gona fiye da 100, amma yanzu gwamnatin ta ɗauki sama da 700 domin tabbatar da ci gaban noma a kananan hukumomi 34 na jihar.
Shi ma a nasa jawabin, Shugaban Shirin Cigaban Al’umma (CDP), Dr. Kamala Kabir, ya bayyana Malaman Gona a matsayin muhimman abokan tafiya wajen cimma nasarar shirin CDP. Ya buƙace su da su haɗa kai da Jami’an Cigaban Al’umma (CDOs) domin tabbatar da manufar ci gaba da ake son cimmawa.
Rahoton Nigerian Post ya nuna cewa an fara gudanar da irin wannan horo a birnin Katsina, inda mahalarta suka fito daga kananan hukumomi 11 da ke karkashin yankin Katsina ta tsakiya, sannan za a ci gaba da gudanar da shi a sauran manyan yankuna biyu na jihar.