HomeSashen HausaFulani Na Ƙoƙarin Ƙwace Garuruwa Da Kuma Gonaki A Yankin Dukku Da...

Fulani Na Ƙoƙarin Ƙwace Garuruwa Da Kuma Gonaki A Yankin Dukku Da Darazo A Jihar Gombe

-

Rahotannin sun bayyana cewa, wasu Fulani suna ƙoƙarin ƙwace wasu garuruwa da ke tsakanin kan iyakar ƙananan hukumomin Dukku (Jihar Gombe) da Darazo (Jihar Bauchi).

Shaidun gani da ido da suka fito daga yankin, su ne suka tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce, fulanin sun tarwatsa al’ummar garin Yau Tare, inda suka ka umarce su da su gaggauta barin garin.

Kamar yadda Nigerian Post ta bibiyi rahoton, dalilin hakan ne ya sa ma zauna garin suka fara ƙaura nan take, bayan sun kashe wani a yayin da suka kai hari garin.

Haka zalika, sun shiga wasu garuruwa kamar Jamari, Dukkuyel a ranakun Kasuwa, inda suka dinga dukkan mutane babu wani dalili.

Tuni dai aka tabbatar da faruwar lamarin, inda aka kara jaddada cewa, Fulanin na yawo tsakanin Yau Tare, Hashidu, Malala, Jamari Dukkuyel da wasu garuruwa, wanda hakan ya jefa al’umma cikin tashin hankali da gudun hijira.

Haka zalika, sun bayyana aniyarsu ta amfani da gonakin al’ummar yankin, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin manoma da iyalai.

Rahotanni kuma na cewa, ana zargin Fulanin da gayyato abokan su daga wasu sassa daban-daban na ƙasar nan domin ƙara ƙarfi, yanzu haka sun sauka cikin dajin Darazo.

Saboda haka ake kira ga gwamnatocin jihohin Gombe da Bauchi da su gaggauta ɗaukar mataki na musamman, domin kare rayuka, gonaki da dukiyoyin jama’a a wannan yanki kafin lamura su rikide zuwa rikicin da zai fi ƙarfin Gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‘Yan Bindigar Da Suka Sace Mutane 3 A Tsakiyar Katsina Sun Nemi Miliyan 600 Kuɗin Fansa

Wasu ’yan bindiga da suka sace wasu ma’aurata da ’yarsu yayin wani hari da suka kai a unguwar Filin Canada da ke Sabuwar Unguwa a...

Hanyoyin Da Matasa Ya Kamata Su Bi Domin Gina Rayuwarsu Tun Kafin Tsufa – Inji Ameer Salisu Yaro

Da yake ƙarin haske kan shawarwarin, ya ce ‎lokacin samartaka da ƙuruciya ba kawai mataki ne na rayuwa kaɗai ba, mataki ne wanda ake gina...

Most Popular