HomeSashen Hausa'Yan Bindigar Da Suka Sace Mutane 3 A Tsakiyar Katsina Sun Nemi...

‘Yan Bindigar Da Suka Sace Mutane 3 A Tsakiyar Katsina Sun Nemi Miliyan 600 Kuɗin Fansa

-

Wasu ’yan bindiga da suka sace wasu ma’aurata da ’yarsu yayin wani hari da suka kai a unguwar Filin Canada da ke Sabuwar Unguwa a cikin birnin Katsina, sun tuntubi dangin wadanda aka sace suna neman kudin fansa har Naira miliyan 600.

Wata majiyar daga cikin dangin wadanda akayi garkuwar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana hakan ga majiyarmu ta jaridar Daily Trust a jiya.

An sace Anas Ahmadu mai shekaru 33, matarsa Halimat, da ’yarsu Jidda, a safiyar ranar Talata.

Rahotannin dai sun bayyana cewa Wani dan sa-kai mai suna Abdullahi Muhammad mai shekaru 25, ya rasa ransa bayan da aka harbe shi yayin da yake kokarin ceto wadanda aka sace daga hannun masu garkuwar da suka tsere kafin zuwan jami’an tsaro.

Majiyar ta bayyana cewa lambar wayar Anas ce aka yi amfani da ita wajen kiran kawun matarsa, Malam Ibrahim, domin neman kudin fansa a jiya.

Sai dai an bayyana cewa sun shaida wa masu garkuwar cewa dangin ba za su iya biya kudin da ake bukata ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Masu Ƙwacen Waya Sun Hallaka Ma’aikaciyar Lafiya A Zariya

Wasu da ake zargin masu kwacen waya ne sun kashe ma’aikaciyar jinya a Asibitin Gambo Sawaba da ke Zariya a jihar Kaduna mai suna Hadiza...

Gwamnan Katsina Ya Zama Abin Koyi Ga Sauran Jihohin Najeriya— Inji Kashim Shettima

Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana cewa, Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya zama abin koyi idan akai duba da...

Most Popular