Wasu ’yan bindiga da suka sace wasu ma’aurata da ’yarsu yayin wani hari da suka kai a unguwar Filin Canada da ke Sabuwar Unguwa a cikin birnin Katsina, sun tuntubi dangin wadanda aka sace suna neman kudin fansa har Naira miliyan 600.
Wata majiyar daga cikin dangin wadanda akayi garkuwar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana hakan ga majiyarmu ta jaridar Daily Trust a jiya.
An sace Anas Ahmadu mai shekaru 33, matarsa Halimat, da ’yarsu Jidda, a safiyar ranar Talata.
Rahotannin dai sun bayyana cewa Wani dan sa-kai mai suna Abdullahi Muhammad mai shekaru 25, ya rasa ransa bayan da aka harbe shi yayin da yake kokarin ceto wadanda aka sace daga hannun masu garkuwar da suka tsere kafin zuwan jami’an tsaro.
Majiyar ta bayyana cewa lambar wayar Anas ce aka yi amfani da ita wajen kiran kawun matarsa, Malam Ibrahim, domin neman kudin fansa a jiya.
Sai dai an bayyana cewa sun shaida wa masu garkuwar cewa dangin ba za su iya biya kudin da ake bukata ba.