Wasu ƴaƴan jam’iyyar PDP da ake ganin ƴan tsagin Ministan Abuja, Nyesom Wike ne sun gudanar da wani taro a daren jiya Litinin a Abuja, inda suka fitar da wasu sharuɗɗa da suka ce suna buƙatar a cika su gabanin babban taron jam’iyyar, wanda za a yi a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamban bana a birnin Ibadan na jihar Oyo.
Kamar yadda majiyar BBC Hausa ta wallafa a shafinta ta ruwaito cewa, a wata sanarwa da suka fitar a yau Talata, mutanen waɗanda suka kira kansu da sunan Eminent Leaders and Concerned Stakeholders of the PDP, sun ce sun amince da tsarin rabon muƙaman jam’iyyar, amma ba za su aminta da ƙara rarraba muƙaman ba zuwa jihohi, bayan rabon a tsakanin yankunan.
Haka kuma sun ce duk da sun amince a bar shugabancin jam’iyyar a Arewa, suna so ne shugaban ya fito daga yankin Arewa ta Tsakiya.
Sauran sharuɗan dai sun haɗa da:
Sake zaɓen shugabannin jam’iyyar a Ebonyi da Anambra.
Sake zaɓen shugabannin jam’iyyar na Kudu maso Gabas.
Amincewa da sakamakon zaɓen shugabannin Kudu maso Kudu da aka yi a Calabar.
Sake zaɓen shugabannin jam’iyyar na ƙananan hukumomi a Ekiti ba tare da ɓata lokaci ba.
Sanarwar dai ta ƙara da cewa idan har aka yi adalci, jam’iyyar PDP za ta magance matsalolin da take fuskanta sannan ta dawo da ƙarfinta a fagen siyasa.