Your message has been sent
Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya Ta (NSCDC) Reshen Jihar Katsina Ta Kama wanda ake zargi da sojan gona amatsayin ma’aikacin hukumar a yan’kin unguwar kwado cikin birnin katsina.
Hakan cikin wata sanarwar manema labarai da jami’in hulda da jama’a na rundunar a katsina S C Buhari Hamisu ya fitar.
Hukumar ta samu labari dangane da wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, inda ake nuna yadda wasu ‘yan unguwar Kwado suka cafke wani mutum mai suna Abdurrashid Gambo, a unguwar Kwado da ke cikin birnin Katsina, a ranar Lahadi, 31 ga watan Agusta, 2025.
Ana zargin Abdurrashid da laifin sata, inda aka kama shi dauke da kayan sanye na hukumar NSCDC. Ya bayyana cewa yana daga cikin ’yan sa-kai na hukumar NSCDC, a ofishin Katsina dake kwaryar ktsina, shekaru shida da suka gabata, kuma yana zaune a unguwar Kofar Durbi layin unguwar Mallam Niga.
Domin bayyana gaskiyar lamarin, hukumar na son jaddada cewa, wannan mutumin ba ya cikin jerin ’yan sa-kai na ofishin NSCDC na Katsina a kowane lokaci.
Hukumar ta yaba matuka da irin kokari, jajircewa da kulawar al’ummar unguwar Kwado wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankinsu.
Har ila yau, hukumar na ci gaba da tabbatar da gaskiya, da’a, da kwaraewa a aikinta waɗanda su ne ginshikan ayyukan rundunar.
Kwamandan rundunar, Ahmad, ya bayyana godiyarsa ga daukacin jama’ar jihar bisa hadin kai da goyon bayan da suke ci gaba da bayarwa, tare da rokon karin goyon baya ta hanyar samar da sahihan bayanai cikin lokaci domin taimaka wa hukumomin tsaro wajen bankado miyagu da masu tada hankalin jama’a a fadin jihar.