HomeLabarai‘Yansandan Katsina Sun Cafke Ƙasurgumin Barawon Mota, Tare Da Ƙwato Toyota Corolla

‘Yansandan Katsina Sun Cafke Ƙasurgumin Barawon Mota, Tare Da Ƙwato Toyota Corolla

-

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Katsina ta ce ta samu nasarar cafke wani mutum da ake zargi da satar mota tare da kwato wata mota kirar Toyota Corolla samfurin 2019 da ake zargin an sace a Abuja.

A cewar rundunar, lamarin ya faru ne a ranar 30 ga watan Agusta, 2025, da misalin ƙarfe 8:00 na safe, inda aka samu bayanan sirri cewa an gano wata mota da aka yi wa wani mazaunin Abuja, Mr. Sunday Solomon Jiyah, fashi da ita tare da wasu kayayyaki masu daraja, a unguwar Kofar Kwaya cikin birnin Katsina.

A cikin sanarwar da ya fitar ga Manema Labarai, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yansanda ta Katsina, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, anipr, ya ce jami’an sashin Anti-Kidnapping Unit suka bi diddigin motar har suka kama wani Muhammad Abdullahi, mai shekaru 28, mazaunin unguwar Kofar Kaura, da ake zargin shi ne ke riƙe da motar.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, wanda ake zargin ya bayyana cewa ya karɓi motar daga wani Abdul da ake kira Dukiya, mazaunin ƙaramar hukumar Malumfashi, wanda yake shahararren mai satar mota ne, inda hukumar ke kan ƙoƙarin kamoshi duk da ya gudu.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Katsina, CP Bello Shehu, ya yaba da ƙwazon jami’an da suka gudanar da aikin, tare da tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da yaki da miyagun laifuka a jihar. Ya kuma roƙi al’umma da su ci gaba da bayar da bayanai cikin lokaci domin taimaka wa hukumomi wajen tabbatar da tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Katsina Police Foil Kidnap Attempt, Rescue 18-Year-Old Girl in Danmusa LG

The Katsina State Police Command has foiled a kidnapping attempt and rescued an 18-year-old girl in Danmusa Local Government Area following a swift response by...

Harin Sojin Sama a Zamfara Ya Hallaka Sama da Mutane 100

A cikin wata sanarwa da rundunar Operation Fansan Yamma ta fitar, ta ce an kai harin ne bayan samun sahihan bayanan sirri da suka nuna...

Most Popular