Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Katsina ta ce ta samu nasarar cafke wani mutum da ake zargi da satar mota tare da kwato wata mota kirar Toyota Corolla samfurin 2019 da ake zargin an sace a Abuja.
A cewar rundunar, lamarin ya faru ne a ranar 30 ga watan Agusta, 2025, da misalin ƙarfe 8:00 na safe, inda aka samu bayanan sirri cewa an gano wata mota da aka yi wa wani mazaunin Abuja, Mr. Sunday Solomon Jiyah, fashi da ita tare da wasu kayayyaki masu daraja, a unguwar Kofar Kwaya cikin birnin Katsina.
A cikin sanarwar da ya fitar ga Manema Labarai, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yansanda ta Katsina, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, anipr, ya ce jami’an sashin Anti-Kidnapping Unit suka bi diddigin motar har suka kama wani Muhammad Abdullahi, mai shekaru 28, mazaunin unguwar Kofar Kaura, da ake zargin shi ne ke riƙe da motar.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, wanda ake zargin ya bayyana cewa ya karɓi motar daga wani Abdul da ake kira Dukiya, mazaunin ƙaramar hukumar Malumfashi, wanda yake shahararren mai satar mota ne, inda hukumar ke kan ƙoƙarin kamoshi duk da ya gudu.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Katsina, CP Bello Shehu, ya yaba da ƙwazon jami’an da suka gudanar da aikin, tare da tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da yaki da miyagun laifuka a jihar. Ya kuma roƙi al’umma da su ci gaba da bayar da bayanai cikin lokaci domin taimaka wa hukumomi wajen tabbatar da tsaro.