An Zargi Sanata Babba Kaita Da Karbar Kudin Aikin Madatsar Ruwa Ta Kankia Har Sau Biyu Kuma Ba’a Yi Aikin Ba
Manoman Rani da ke harkokin noma a madatsar ruwa ta Kankia, sun koka akan halin da Tsohon Sanatan Shiyyar Daura Sanata Ahmed Babba Kaita ya sanya madatsar ruwan, wanda ya karbi kudin yashe ta kuma bai gudanar da aikin ba.
Manoman da wasu ‘yan kishin ƙasa ‘yan asalin yankin ne suka mika koken su ga Manema Labarai da suka ziyarci madatsar ruwan.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, kamar yadda suka bayyana, tun lokacin yana Dan Majalissar Tarayya ya ƙaddamar da fara aikin yashe magudanar ruwan karo na farko, amma ko kashi 1 cikin goma ba’a yi ba na aikin aka kwashe kayan aiki.
Haka kuma, karo na biyu ma yana Sanatan Shiyyar Daura ya ƙaddamar da aikin yashe Dam din, a nan ma daga baya aka kwashe kayan aikin bayan saukar damina, kuma ba’a cigaba da aiwatar da shi ba. Tuni dai suka buƙaci a bi kadin dalilin da ya sanya bai yi aikin ba bayan karbar kuɗin har sau biyu.
A cewar su, wannan yaudara biyu da Sanata Babba Kaita ya yi ma su, ya kawo koma baya ga rayuwar su, domin madatsar ruwan ta bar ajiye ruwa Kwata-kwata, baya ga yankewar katangar ta da ke haifar da ambaliyar ruwa a kowace shekara.
Sun jaddada cewa, ka a wannan shekarar, madatsar ruwan ta haifar da ambaliya ruwa da ya yi sanadiyar rugujewar gidajen sama da 50 a Unguwar Layi da ke cikin garin Kankia.
Rahoton ya tabbatar da cewa, garuruwan da ruwa ke ma barazana sun haɗa da, Ƙauyen Maina, Gandi, Fanga, Kauyen Dawa, Kafin Dangi, Zango, Malabare, Dannayaki, Daurawa, da kuma wani yanki cikin garin Kankia.
A sabili da haka manoman rani da yan kishin ƙasa a yankin ke yin kira ga Gwamnatin Jiha da ta Tarayya a kan su bi kadin wannan aiki da suka zargi Sanata Ahmed Babba Kaita da karba har sau biyu kuma ba’a yi ba.