Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Maryam Sanda afuwa — matar da aka yankewa hukuncin kisa a shekarar 2020 bayan samunta da laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello.
Maryam Sanda, mai shekaru 37, ta shafe shekaru shida da watanni takwas tana tsare a gidan gyaran hali na Suleja kafin wannan afuwa daga shugaban ƙasa.
Mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan shawarar kwamitin shugaban ƙasa kan yafewa fursunoni da masu laifi bayan nazarin takardun shari’arsu da yanayin da suke ciki.