Shugaban ƙungiyar kananan hukumomi ta ƙasa (ALGON), reshen Jihar Edo, Sunny Ekpetika Ekpeson, ya umarci shugabannin kananan hukumomi 18 da ke cikin jihar su tabbatar da cewa ma’aikatan su na saka hula mai ɗauke da tambarin Shugaba Bola Tinubu yayin tarurruka da kuma zaman ofis a sakateriyoyin kananan hukumomi.
Jaridar LEADERSHIP ta rawaito cewa Ekpeson, ya ce wannan umarni ya shafi Kansila masu gafaka (Supervisory Councillors), mataimakan musamman (SSAs). Ya ce, wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin nuna goyon bayan jama’a daga ƙasa ga gwamnatin Shugaba Tinubu da manufofinsa na siyasa a Jihar Edo.
Yayin da yake bayyana dalilin wannan umarni a ƙarshen mako, ta cikin wata sanarwa da mai taimaka masa wajen yada labarai, Agbukor Lucky Apeakhuye, ya fitar, shugaban ALGON ɗin ya bayyana cewa wannan shiri ya samo asali ne daga saƙon da Gwamnan Jihar Edo, Sanata Monday Okpehbolo, ya jaddada kwanan nan na neman haɗin kai a siyasa.
Ya jaddada cewa nuna alamomin siyasa a matakin ƙananan hukumomi na da muhimmanci wajen ƙarfafa goyon baya ga Shugaba Tinubu yayin da ake shirin babban zaɓen 2027.
“Ayyukan da suka nuna goyon baya daga ƙananan hukumomi za su taimaka wajen cimma burin sama da ƙuri’u miliyan 3.5 da Jihar Edo ta yi wa Shugaba Tinubu alkawari.
“Dole ne mu fara gina wannan kuzari tun daga matakin ƙasa yanzu, ciki har da alamomin nuna ɗa’a da sadaukarwa a siyasa,” in ji shi.