Rundunar Sojin Sama ta Ƙasa ta ce ta ƙaddamar da luguden wuta mai ƙarfi a Arra, wani sanannen mafakar ƴan ta’adda a Sambisa.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a da Bayar da Bayanai, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar a jiya Laraba a Abuja.
Ya ce an gudanar da luguden ne bayan umarnin da Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke, ya bayar.
Ejodame ya ce an kai harin ne bayan bayanan sirri da sa ido da kuma bincike da suka gano motsin ‘yan ta’adda bayan kwanton ɓaunar da aka yi a Kashomri ranar 17 ga Oktoba.
