HomeSashen HausaGwamna Radda Ya Haramta Rufe Lambar Ababen Hawa A Katsina

Gwamna Radda Ya Haramta Rufe Lambar Ababen Hawa A Katsina

-

Gwamnatin Jihar Katsina ta fitar da sabon umarni na hana duk wani mai mota ko babur rufe lambar abin hawan sa, tare da bada umarnin kame duk wanda aka samu yana aikata hakan ba tare da babban uzuri ba.

 

Kamar yadda Nigerian Post ta bibiyi rahoton, dokar ta shafi kowa da kowa, da suka haɗa da jami’an gwamnati da al’umma gaba ɗaya a duk faɗin jihar.

 

A cewar sanarwar, gwamnati ta ɗauki wannan mataki ne domin kama Masu rufe lamba, wanda idan aka bar su hakan na iya zama barazana ga tsaro, musamman wajen ɓoyewa ko gudun kamun masu aikata laifuka.

 

Tuni dai dokar ta fara aiki nan take, inda Gwamna Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, ya umurci Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Katsina da sauran hukumomin zirga-zirga su tabbatar da aiwatar da wannan doka domin kare tsaron jihar.

 

An kuma shawarci jama’a da su bi doka da oda bisa ga sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar, Abdullahi Garba Faskari, ya sanya wa hannu, domin kauce wa hukunci.

 

Wannan umarni na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar, Ibrahim Almu Gafai, ya rabawa manema labarai a ranar Laraba, 10 ga Disamba, 2025.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Jaruma Rahama Sadau, Ta Shirya Bikin Fina-finan Arewacin Najeriya

Fitacciyar jaruma a masana’antar Kannywood da Nollywood, Rahama Sadau, ta shirya bikin ɗaga darajar fina-finan Arewacin Najeriya.   Jarumar ta ce ta shirya bikin ne domin tallata...

‎Malami Ya Zargi DSS da Tauye Masa ’Yancin Kare Kansa a Kotu

‎Tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami (SAN), ya zargi Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da daukar matakan hana shi cikakken...

Most Popular