Mataimakin Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo, ya yanke jiki ya fadi yayin da yake tsaka da gudanar da ayyukansa a ofis ɗinsa da ke Gidan Gwamnati, Yenagoa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Shaidu daga fadar gwamnati sun ce lamarin ya faru ne ba wani manuniyar cewa yana da wata rashin lafiya, lamarin da ya jefa ma’aikatan ofishin cikin tashin hankali.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an gaggauta kai Mataimakin Gwamnan zuwa Babban Asibitin Tarayya da ke Yenagoa (Federal Medical Centre) domin kula da lafiyarsa.
Duk da cewa hukumomin jihar ba su fitar da cikakken bayanin halin da yake ciki ba tukuna, majiyoyi sun ce likitoci suna ci gaba da aiki tukuru don tabbatar da ya farfaɗo.
