Rikicin da ke damun Katsina United ya kara kamari jiya da yamma, bayan da ‘yan wasan kulob ɗin suka gudanar da zanga-zangar neman a biya su albashin watanni biyar da suka dade suna bi.
Majiyarmu ta jaridar the Nation ra ruwaito cewa Lamarin ya faru ne jim kadan kafin fafatawa mako na 16 a Gasar NPFL da Bendel Insurance, wadda suka sha kashi 1–0 daga baya.
Rikicin ya faru ne a sansanin su na Ilorin, inda ‘yan wasan da suka gaji da jinkiri suka hana motar su ta tashi zuwa filin wasa na George Innih, Ilorin — wurin da zasu buga wasan.
Yan’wasa da suka gudanar da zanga-zangar sun nace cewa ba za su fito wasa ba sai an warware batun bashin albashin da suke bin kulob ɗin, wanda wasu daga cikinsu ke cewa tun farkon kakar bana ake binsu.
Wannan takaddama ta tilasta wa jami’an kulob ɗin shirin gaggawa, inda a ƙarshe suka samo wata mota daban domin kai ‘yan wasan da ake da su zuwa filin wasa.
Bendel Insurance ta yi amfani da wannan rudani, inda a minti na 72 Elmer Arunta ya zura kwallo cikin natsuwa, wanda ya tabbatar musu da nasarar farko a waje a wannan kakar tare da ficewa daga yankin waɗanda ke fuskantar faduwa rukuni.
