HomeSashen HausaTinubu Ya Ƙara Jaddda Umarnin Janye ’Yansanda Daga Gadin Manyan Mutane

Tinubu Ya Ƙara Jaddda Umarnin Janye ’Yansanda Daga Gadin Manyan Mutane

-

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce ba za a sassauta umarnin janye ’yansanda daga gadin manyan jami’ai ba, yana mai gargadin dukkan ministoci su bi umarnin nan take.

 

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar a yau Laraba.

 

A yayin taron majalisar zartarwa ta kasa, da aka gudanar a Abuja, Tinubu ya umarci mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu, Ministan Harkokin ’Yansanda Ibrahim Gaidam, da IG Kayode Egbetokun su tabbatar da an aiwatar da matakin.

 

Ya ce aikin ’yansanda shi ne kare al’umma, kuma za a maye gurbin su da jami’an Civil Defence wajen gadin manyan mutane.

 

Shugaban kasar ya ce sake tura ’yansanda aiki a fagen yaki da ’yan bindiga, garkuwa da mutane da ta’addanci zai inganta tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Amurka Ta Ƙwace Wani Babban Jirgin Dakwan Mai Na Najeriya

Dakarun tsaron gabar tekun Amurka da ke aiki tare da sojojin ruwan ƙasar, sun kama wani babban jirgin ruwa na Najeriya da ake kira da...

Gwamna Radda Ya Ƙaddamar da Majalisar Sarakunan Jihar Katsina

Gwamna Radda Ya Ƙaddamar da Majalisar Sarakunan Jihar Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, Ph.D, CON, ya kaddamar da Majalisar Sarakunan Jihar Katsina, inda...

Most Popular