HomeSashen HausaZanga-zangar Adawa Da Juyin Mulki Ta Ɓarke A Guinea-Bissau

Zanga-zangar Adawa Da Juyin Mulki Ta Ɓarke A Guinea-Bissau

-

Daruruwan ‘yan Guinea-Bissau sun yi tattaki a cikin birnin Bissau, babban birnin ƙasar, domin yin zanga-zanga kan juyin mulkin soja da aka yi a watan da ya gabata tare da neman a saki shugabannin ‘yan adawa.

 

Masu zanga-zangar sun yi arangama da jami’an tsaro a ranar Juma’a yayin da suke kiran a saki Domingos Pereira, shugaban Jam’iyyar African Party for the Independence of Guinea and Cape Verde (PAIGC), wanda rahotanni suka ce an tsare shi ne a lokacin juyin mulkin.

 

Jami’an soji sun sanar da juyin mulki a ƙasar da ke Yammacin Afirka mai amfani da harshen Fotigal, kwanaki kaɗan bayan gudanar da zaɓen shugaban ƙasa, kuma ‘yan sa’o’i kaɗan kafin a ayyana sakamakon zaɓen.

 

Shugaba Umaro Embaló da babban abokin hamayyarsa, Fernando Dias da Costa, duk sun ayyana kansu a matsayin waɗanda suka yi nasara tun kafin hukumar zaɓe ta sanar da sakamakon.

 

Daga bisani, ‘yan juyin mulkin sun naɗa Manjo Janar Horta Inta-a a matsayin shugaban riƙo.

 

Bayan juyin mulkin, Ƙungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta dakatar da Guinea-Bissau daga ƙungiyar har sai an dawo da tsarin mulki a ƙasar.

 

Ƙungiyar ta bayyana wannan mataki ne a cikin wata sanarwa bayan kiran wani taron gaggawa na shugabannin ƙasashe da gwamnatoci ta kafar intanet kan halin da ake ciki.

 

Ana sa ran shugabannin yankin za su gana a ranar Lahadi domin tattauna rikicin da kuma ɗaukar matakan takunkumi masu yuwuwa kan ƙasar ta Yammacin Afirka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‎‘Yanbindiga Sun Hallaka Mutane 20, Sun Kone Rabin Wani Gari a Katsina

Aƙalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu a garin Doma, dake Karamar Hukumar Faskari, dake cikin Jihar Katsina, bayan da ’yan bindiga dauke da manyan...

Jami’an da Aka Kama Kan Yunkurin Juyin Mulki Za Su Ɗanɗana Kuɗarsu– Ministan Tsaro 

Ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa, ya ce jami’an sojojin da aka kama bisa zargin yunkurin juyin mulki da aka dakile sun san sakamakon abin da...

Most Popular