HomeLabaraiZanga-zangar Adawa Da Juyin Mulki Ta Ɓarke A Guinea-Bissau

Zanga-zangar Adawa Da Juyin Mulki Ta Ɓarke A Guinea-Bissau

-

Daruruwan ‘yan Guinea-Bissau sun yi tattaki a cikin birnin Bissau, babban birnin ƙasar, domin yin zanga-zanga kan juyin mulkin soja da aka yi a watan da ya gabata tare da neman a saki shugabannin ‘yan adawa.

 

Masu zanga-zangar sun yi arangama da jami’an tsaro a ranar Juma’a yayin da suke kiran a saki Domingos Pereira, shugaban Jam’iyyar African Party for the Independence of Guinea and Cape Verde (PAIGC), wanda rahotanni suka ce an tsare shi ne a lokacin juyin mulkin.

 

Jami’an soji sun sanar da juyin mulki a ƙasar da ke Yammacin Afirka mai amfani da harshen Fotigal, kwanaki kaɗan bayan gudanar da zaɓen shugaban ƙasa, kuma ‘yan sa’o’i kaɗan kafin a ayyana sakamakon zaɓen.

 

Shugaba Umaro Embaló da babban abokin hamayyarsa, Fernando Dias da Costa, duk sun ayyana kansu a matsayin waɗanda suka yi nasara tun kafin hukumar zaɓe ta sanar da sakamakon.

 

Daga bisani, ‘yan juyin mulkin sun naɗa Manjo Janar Horta Inta-a a matsayin shugaban riƙo.

 

Bayan juyin mulkin, Ƙungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta dakatar da Guinea-Bissau daga ƙungiyar har sai an dawo da tsarin mulki a ƙasar.

 

Ƙungiyar ta bayyana wannan mataki ne a cikin wata sanarwa bayan kiran wani taron gaggawa na shugabannin ƙasashe da gwamnatoci ta kafar intanet kan halin da ake ciki.

 

Ana sa ran shugabannin yankin za su gana a ranar Lahadi domin tattauna rikicin da kuma ɗaukar matakan takunkumi masu yuwuwa kan ƙasar ta Yammacin Afirka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

ADC Ta Zargi Tinubu Da Raba Kan ‘Yan Adawa Ta Hanyar NDC

Jam’iyyar ADC ta yi zargin cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC na da hannu wajen ƙirƙirar sabuwar jam’iyyar NDC domin raunata haɗin...

Vinicius Jr Accused of Reporting Teammates to Madrid Chiefs

Vinicius Jr Accused of Reporting Teammates’ Issues to Real Madrid Chiefs. Reports from several European media outlets claim that Vinícius Júnior is being accused of informing...

Most Popular