Babbar Mai Shari’a ta Nijeriya, Justice Kudirat Kekere-Ekun, ta bayyana cewa umarnin Shugaban kasa na janye jami’an ‘yan sanda da ke aiki a matsayin masu gadin Manyan Mutane (VIPs) na daga cikin matakan da gwamnati ke dauka domin dakile karuwar matsalar rashin tsaro a kasar.
Ta bayyana hakan ne a matsayin wani bangare na kokarin mayar da karfin ‘yan sanda inda ya fi dacewa, musamman wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin Nijeriya.
Sai dai mai taimaka wa Babbar Mai Shari’a ta Nijeriya kan harkokin yada labarai, Tobi Soniyi, ya bayyana cewa wannan umarni ba ya shafar alkalai, inda ya jaddada cewa tsaron masu shari’a bai shiga cikin wannan mataki ba.
