HomeSashen HausaBan Da Alƙalai A Jerin Waɗanda Za a Cire Wa 'Yansandan Da...

Ban Da Alƙalai A Jerin Waɗanda Za a Cire Wa ‘Yansandan Da Ke Ba Su Kariya a Najeriya– Inji Alkalin Alkalai

-

Babbar Mai Shari’a ta Nijeriya, Justice Kudirat Kekere-Ekun, ta bayyana cewa umarnin Shugaban kasa na janye jami’an ‘yan sanda da ke aiki a matsayin masu gadin Manyan Mutane (VIPs) na daga cikin matakan da gwamnati ke dauka domin dakile karuwar matsalar rashin tsaro a kasar.

Ta bayyana hakan ne a matsayin wani bangare na kokarin mayar da karfin ‘yan sanda inda ya fi dacewa, musamman wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin Nijeriya.

Sai dai mai taimaka wa Babbar Mai Shari’a ta Nijeriya kan harkokin yada labarai, Tobi Soniyi, ya bayyana cewa wannan umarni ba ya shafar alkalai, inda ya jaddada cewa tsaron masu shari’a bai shiga cikin wannan mataki ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Nijeriya Ta Musanta Zargin Leken Asiri Kan Jirginta Da Ke Burkina-Faso

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta karyata jita-jitar da ke cewa jirginta kirar C-130 da ya sauka ba tare da shiri ba a Bobo-Dioulasso,...

Duniya Za Ta Fuskanci Ƙalubale, Idan Najeriya Ta Wargaje– Inji Sanata Kashim Shettima

Mataimakin Shugaban Ƙasa a Najeriya, Kashim Shettima ya ce gwamnatin Tinubu ba za ta taɓa bari Najeriya ta ruguje a hannunta ba, komai rintsi.   Kamar yadda...

Most Popular