HomeSashen Hausa‎Bello Turji Ya Tabbatar da Cewa Sun Saba Ganawa da Tsohon Gwamnan...

‎Bello Turji Ya Tabbatar da Cewa Sun Saba Ganawa da Tsohon Gwamnan Zamfara Matawalle

-

Fitaccen jagoran ‘yan bindiga da ake nema ruwa a jallo, Bello Turji, ya tabbatar da cewa ya taba shiga tattaunawar sulhu da jami’an gwamnatin Jihar Zamfara a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle, wanda a halin yanzu shi ne Karamin Ministan Tsaro.

‎Sai dai Turji ya musanta zargin da ke cewa an ba shi Naira miliyan 30 a matsayin wani bangare na yarjejeniyar sulhun.

‎A cikin wani saƙon murya (audio) da ke yawo a kafafen sada zumunta, Turji ya karyata ikirarin da Musa Kamarawa, tsohon mai shiga tsakanin sulhun da gwamnatin Zamfara, inda ya bayyana batun kudin a matsayin karya tsagwaron gaske.

‎Wallahi tun daga ranar da aka haife ni ban taba mallakar ko Naira miliyan biyar ba,” in ji Turji. “Abin da muke yi ba don amfanin kaina ba ne. Ba a taba ba mu wannan Naira miliyan 30 da kake magana a kai ba.”

‎Turji ya ce ganawar da ya yi da jami’an gwamnatin jihar na cikin yunkurin samar da zaman lafiya, kuma ya jaddada cewa bai amfana da ko sisi ba daga wannan tsari. Ya zargi Musa Kamarawa da bayar da shaidar karya tare da cin amanar amincewar da aka gina yayin tattaunawar.

‎“Mun amince da zaman lafiya ne lokacin da gwamnatin Zamfara ta nada ka,” in ji shi. “Amma abin da kake fada yanzu cike yake da karya. Ban karɓi ko Naira miliyan uku ba.”

‎Jagoran ‘yan bindigar ya kuma zargi wasu tsofaffin shugabannin siyasa a jihohin Zamfara da Sakkwato, tare da ambaton Sanata Ahmed Sani Yerima, da cewa su ne suka taimaka wajen hura wutar rikici, ta hanyar bai wa wasu kungiyoyi makamai da kuma karfafa kafa ‘yan sa-kai da ke kai hare-hare kan al’ummomin Fulani.

‎“Muna fadin gaskiya a fili cewa tsofaffin gwamnonin Zamfara da Sakkwato tare da Ahmed Sani Yerima su ne ke da alhakin masifun da suka afkawa wadannan jihohi,” in ji Turji, inda ya bukaci a kama su tare da gudanar da bincike a kansu.

‎A sakon nasa, Turji ya yi kokarin kare kansa, yana mai cewa abin da yake yi ya samo asali ne daga matsalar tsaro da zalunci, ba wai don wata manufa ta siyasa ba.

‎“Ba ‘yan siyasa ba ne mu, kuma ba kayan aikin ‘yan siyasa ba ne,” in ji shi. “Babu wani mutum da ke daukar nauyinmu.”

‎Duk da haka, Turji, wanda aka danganta shi da kisan kiyashi, garkuwa da mutane, da tilastawa dubban jama’a barin muhallansu a Zamfara da makwabtanta, bai yi magana kai tsaye kan zarge-zargen hare-haren da ake danganta wa kungiyarsa ba.

‎Sai dai ya ce yana kare kansa ne kawai, yana mai cewa yana magana ne “a gaban Allah shi kadai.”

‎Hukumomin tsaro na Najeriya sun sha bayyana Bello Turji a matsayin daya daga cikin mafi hatsarin jagororin kungiyoyin dauke da makamai a yankin Arewa maso Yamma, inda rundunar soji ta taba ayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo bisa laifukan ta’addanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‎Dangote Ya Buƙaci a Binciki Shugaban NMDPRA Kan Zargin Ɓarnatar Da Kuɗaɗe ‎

Hamshakin ɗan kasuwar nan, Alhaji Aliko Dangote, ya yi kira da a gudanar da bincike kan Shugaban Hukumar Kula da Man Fetur na Ƙasa (NMDPRA),...

An Ƙone Wata Matar Aure Da Ɗanta A Kano 

Mazauna unguwar Sheka Sabuwar Gandu da ke cikin birnin Kano, sun shiga firgici a ranar Lahadi bayan kisan wata mata mai juna biyu da ɗanta...

Most Popular