Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya Ta Buƙaci A Gaggauta Bincike Mai Zurfi Kan Zargin Da Ake Yiwa Matawalle Da Alaƙa Da Yan Bindiga
Ƙungiyar Coalition of Northern Groups (CNG) ta bayyana damuwa mai tsanani kan ikirarin da Musa Kamarawa, tsohon mataimaki na musamman ga tsohon Gwamnan Zamfara kuma Ministan Tsaron Ƙasa na yanzu, Bello Matawalle, ya yi a wani faifan bidiyon da yake nuna Matawallen na da alaƙa da tallafawa yan bindiga.
CNG ta ce zargin ya shafi tura kuɗi kai tsaye ga fitaccen shugaban ‘yan bindiga Bello Turji, sayen motocin Hilux da dama ga ƙungiyoyin ta’addanci, da kuma bayar da tallafin kayan aiki kamar gidaje, shanu da sauran dukiya, wanda ake zargin ‘yan siyasa daga Zamfara da maƙwabtanta suka taimaka wajen aiwatarwa.
A cewar CNG, waɗannan ikirari suna nuna yiwuwar alaƙa mai zurfi tsakanin wasu manyan jami’an gwamnati da ‘yan bindiga, lamarin da ka iya rusa ƙoƙarin sojoji tare da ƙara jefa al’umma cikin haɗari.
Ƙungiyar ta ce irin waɗannan zarge-zarge ba za a iya watsi da su ta hanyar musantawa kawai ba, domin hakan na ƙara haifar da shakku cewa ana ɓoye gaskiya.
CNG ta kuma soki matakin Ministan na kai ƙara kan Sheikh Murtala Asada, tana mai cewa hakan na iya zama yunƙurin hana faɗin gaskiya, maimakon kare mutunci. Ta bukaci Sheikh Asada da ya fito da dukkan hujjojin da ke hannunsa ba tare da tsoro ba.
Ƙungiyar ta jaddada cewa babu wanda ya isa ya fi karfin doka, kuma ɓoye masu hannu a ta’addanci na raunana tsaro da amincewar jama’a.
Saboda haka, CNG ta nemi bincike mai zaman kansa, binciken da babu son zuciya, wanda Majalisar Ƙasa, hukumomin tsaro da Ofishin Babban Lauyan Ƙasa za su jagoranta, domin binciken kuɗaɗe, kayan aiki, sadarwa da duk wata shawara da ka iya taimaka wa ‘yan bindiga.
Ta ce dole a kare masu fallasa gaskiya, kuma duk jami’in gwamnati da aka samu da laifi ya fuskanci hukunci ba tare da la’akari da matsayinsa ko ƙarfin ikonsa ba.
CNG ta jaddada cewa Arewa ta sha wahala matuƙa sakamakon ‘yan bindiga, kuma wannan lokaci wata dama ce ta fuskantar tushen matsalar. Kare masu aikata laifi zai lalata makomar tsaro da amincewar jama’a. Lokacin ɓoyewa ya wuce, lokacin gaskiya da adalci ya yi.
Sa Hannun: Comr Jamilu Aliyu Charanchi, National Coordinator CNG
