Hamshakin ɗan kasuwar nan, Alhaji Aliko Dangote, ya yi kira da a gudanar da bincike kan Shugaban Hukumar Kula da Man Fetur na Ƙasa (NMDPRA), Farouk Ahmed, bisa zargin ɓarnatar da dukiyar jama’a da kuma cutar da tattalin arzikin ƙasa.
Dangote ya bayyana cewa ko shi da irin arzikin da Allah ya hore masa, ba zai iya biyan kuɗin karatun sakandaren ’ya’yansa da ya haura Naira biliyan bakwai ba. Ya ce irin wannan adadi na kuɗi ya wuce tunanin biyan kuɗin makaranta a matakin sakandare.
Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa, ya yi wannan furuci ne cikin wani bidiyo da ya raba wa manema labarai, wanda ya yaɗu a shafukan sada zumunta a ƙarshen makon da ya gabata.
A cewarsa, “Shugaban Hukumar Man Fetur ta NMDPRA, Farouk Ahmed, na biyan kuɗin makarantar sakandaren ’ya’yansa har dala miliyan biyar a Switzerland.”
Wannan furuci ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a, inda da dama ke kira ga hukumomi da su yi cikakken bincike domin tabbatar da gaskiyar zarge-zargen da kuma kare muradun tattalin arzikin ƙasar.
