Gwamna Radda Ya Ƙaddamar da Majalisar Sarakunan Jihar Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, Ph.D, CON, ya kaddamar da Majalisar Sarakunan Jihar Katsina, inda aka nada Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman, a matsayin Shugaban Majalisar.
Haka kuma, Gwamnan ya sanar da Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar-Faruk, a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar. An nada Sanata Ibrahim Idah, Wazirin Katsina, a matsayin Sakataren Majalisar, yayin da Alhaji Sada Salisu-Ruma, Danwairen Katsina, zai rike mukamin Mataimakin Sakatare.
Gwamna Radda ya bayyana cewa Majalisar ta kunshi dukkan masu zaben sarki a fadin masarautun jihar, masu rike da mukaman gargajiya da wadanda ba su da irinsu Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Abdullahi Faskari.
Gwamnan ya bayyana ayyukan Majalisar da suka hada da ba Gwamnatin Jihar shawara kan dokokin Musulunci da na gargajiya, harkokin al’adu, da dangantakar zaman lafiya tsakanin al’umma. Haka kuma, Majalisar na da ikon taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro da doka a fadin jihar idan bukata ta taso.
Shi ma da yake jawabi a madadin sabuwar Majalisar, Sakataren, Sanata Idah, ya yabawa Gwamna bisa amincewar da ya nuna musu, tare da ba da tabbacin cikakken hadin kai da goyon baya ga Gwamnatin Jihar wajen kare muradun majalisun masarauta, gwamnati da al’ummar Jihar Katsina baki daya.
Sauran ayyukan Majalisar dai, sun haɗa da tallafa wa cibiyoyin gargajiya, bunƙasa al’adu da ci gaban al’umma, taimakawa hukumomin haraji wajen tattara kudaden shiga, bayar da gudunmawa wajen kiyaye dazuzzuka da kare muhalli, da kuma kula da ayyukan tsaftar muhalli na lokaci-lokaci a cikin al’umma.
Jerin Mambobin Majalisar Sarakunan Jihar Katsina Sun Haɗa da:
1. Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman – Shugaban Majalisa (Sarkin Katsina)
2. Alhaji Faruk Umar-Faruk – Mataimakin Shugaban Majalisa (Sarkin Daura)
3. Sanata Ibrahim Idah – Sakatare (Wazirin Katsina)
4. Alhaji Sada Salisu-Ruma – Mataimakin Sakatare (Danwairen Katsina)
5. Alhaji Abdullahi Faskari – Mamba (Sakataren Gwamnatin Jihar)
6. Dahiru Barau-Mangal – Mamba
7. Baba Buhari Walin Daura – Mamba
8. Sheikh Yakubu Musa – Mamba
9. Sheikh Naziru Kofar-Waru – Mamba
10. Abdul’aziz Abdul’aziz – Mamba
11. Dukkan masu zaben sarakuna a fadin masarautun jihar – Mambobi
12. Masu rike da mukaman gargajiya a fadin masarautun jihar – Mambobi
13. Sai wasu mutane wanda basuda muƙaman gargajiya.
