HomeSashen HausaNSCDC Ta Ƙara Karfafa Hulda Da Rundunar Sojin Saman Nigeria A Katsina

NSCDC Ta Ƙara Karfafa Hulda Da Rundunar Sojin Saman Nigeria A Katsina

-

Rundunar Tsaron Nijeriya ta (NSCDC) reshen Jihar Katsina tare da Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya, 213 Forward Operating Base Katsina, sun ƙarfafa haɗin gwiwarsu domin tinkarar ƙalubalen tsaro a jihar.

 

Wannan ya fito fili ne yayin ziyarar ban girma da Shugaban Sashen Rundunar Sama na Haɗin Gwiwa, Operation Fansan Yamma Sector 2, wanda kuma shi ne Kwamandan 213 FOB NAF a Katsina, Air Commodore CE Illoh DSS, ya kai wa Kwamandan NSCDC na Jihar Katsina, Commandant of Corps AD Moriki, a ranar Laraba 17 ga Disamba, 2025, a Babban Hedikwatar Rundunar NSCDC da ke Katsina.

 

Nigerian Post ta bibiyi cewa, Kwamandan ya jaddada kyakkyawar alaƙar aiki da ke tsakanin Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya da NSCDC a jihar. Ya ƙara da cewa NSCDC muhimmin abokin hulɗa ne wajen inganta tsaro da kare Muhimman Kadarorin Ƙasa da Ginshikan More Rayuwa.

 

“NSCDC na da matsayi na musamman da muhimmanci wajen tsaron cikin gida da kuma kare Muhimman Kadarorin Ƙasa da Ginshikan More Rayuwa,” in ji Kwamandan.

 

Air Commodore Illoh ya kuma bayyana muhimmancin musayar sahihan bayanan sirri, da ƙarfafa haɗin kai da aiki tare a dukkan matakai na hukumomin tsaro.

 

A nasa jawabin, Commandant Moriki ya yaba da ƙoƙarin Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar jihar.

 

Commandant Moriki ya jaddada kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin hukumomin tsaron biyu a jihar, tare da tabbatar da ƙara ƙaimi wajen haɗin gwiwa da aiki tare.

 

Daga cikin abubuwan da suka gudana yayin ziyarar akwai duba girmamawar runduna (quarter guard), miƙa kyaututtukan tunawa.

 

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar Buhari Hamisu, ya fitar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‎Lokacin Gwamnatin Babana, Sabi’u Tunde Ya Yi Ƙarfin Da Ministoci Tsoron sa Suke– Inji Fatima Buhari

Fatima Buhari, ‘yar fari ga marigayi Muhammadu Buhari, ta ce Tunde Sabiu, tsohon sakataren shugaban ƙasa, yana da babban tasiri a lokacin mulkin mahaifinta ta...

‎Gwamnan Kano Ya Yabawa Tinubu da Abba Bichi Kan Aikin Titin Wuju-Wuju a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana matukar godiyarsa ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu bisa amincewar da ya bayar na sa hannun Gwamnatin...

Most Popular